Buɗe shafukan ayoyi ta hanyar sunan sura da lambar aya
Buɗe shafuka ta hanyar jerin surori da juzu’ai
Karanta ayoyi cikin sauti da muryar sheikh alhuzaifi
Samun damar bincike cikin ayoyin alkur’ani
Samun damar bincike cikin tafsiri da fassara
Samun damar kwafar ayoyi da yaɗa su ko yaɗa adreshin shafin
Samun damar tura ƙorafi a kan tafsirin
Bayanin surorin makkah da madina, tare da bijiro da adadin ayoyin surar, da abinda take karantarwa a farkon kowace sura
Rarraba ayoyin kowace sura gwargwadon abinda suke karantarwa
Bijiro da tafsiri cikin yaren hausa daga littafin “Audahu al- bayan Lima’aani wa Hidayaati Alkur’an” wallafar sheikh, Dr. Muhammad Sani Umar Musa
Tafsiri ne me saukin fahimta, ya kuɓuta daga kalmomi masu zurfin ma'ana, da keɓantattun babuka, don samar da madogara mai sauƙi wajen fahimtar abinda wahayi ya ƙunsa
Bijiro da fassarar ma’anonin Alƙur’ani; kowace aya a keɓance domin sauƙaƙe fahimtar ayoyin, gabanin bijiro da tafsirin wani adadi na ayoyin a haɗe
Taƙaituwa da fassarar ma’anar ayoyi ba tare da ambaton ma’anar kalmomi ba