98-Suratul Bayyina
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
A wasu littattafan tafsiri da masahifu an kira ta da ‘Suratul Bayyina’. A wasu kuma da dama an kira ta ‘Suratul Ƙayyima’.
Annabi (ﷺ) ya kira ta da ‘Lam Yakunil Lazina Kafaru’.
An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Ubayyu ɗan Ka’ab (Allah ya kara masa yarda): “Lalle Allah ya umarce ni in karanta maka ‘Lam Yakunil Lazina Kafaru’.” Sai Ubayyu ya ce: “Ya kuma kama maka sunana?” Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “E.” Sai Ubayyu ya fashe da kuka. [Bukhari #3809 da Muslim #799].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna ganin Sura ce Madaniyya. Amma akwai masu cewa Makkiyya ce. Maganar farko dai ta fi yawa ta kuma fi ƙarfi.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta ɗari da ɗaya (101) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratuɗ Ɗalaƙ’ kafin ‘Suratul Hashri’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta takwas ne (8) a wurin yawancin malamai. Amma a wurin mutanen Basra ayoyinta tara ne (9).
5. Babban Jigonta:
Tana bayanin matsayin manzancin Annabi (ﷺ) da bayyanarsa a fili da kamalar ɗabi'unsa.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Gargaɗin ma’abota littafi da mushirikai game da ƙaryata Alƙur’ani da Manzon Allah (ﷺ).
• Fito da tufka-da-warwara ta mushirikai da ma’abota littafi waɗanda suka kasance suna jiran su ga wata bayyananniyar hujja kafin su yi imani. To yayin da hujjar ta zo musu sai suka kafirce mata.
• Ƙaryata da’awarsu ta cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya wajabta musu su ci gaba da riƙo da addinansu.
• Yi musu narko da azabar lahira.
• Yabon waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, da yi musu alƙawarin samun ni’imar Aljanna ta har abada.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Waɗanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai ba su zamanto masu barin abin da suke kai (na kafirci) ba har sai hujja bayyananniya ta zo musu.
2. (Watau) Manzo daga Allah da zai riƙa karanta (musu) takardu masu tsarki.
3. (Waɗanda) a cikinsu akwai hukunce-hukunce masu ƙima.
4. Waɗanda kuma aka bai wa littafi ba su rarraba ba sai bayan da hujja bayyananniya ta zo musu.
5. Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa ɓarna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miƙaƙƙiyar hanya.
6. Lalle waɗanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafiya sharrin halitta.
7. Lalle waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, waɗannan su ne mafiya alherin halitta.
8. Sakamakonsu a wajen Ubangijinsu gidajen Aljanna ne na dawwama waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu har abada; Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Wannan kuma (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da bayyana cewa, kafirai daga cikin Yahudawa da Nasara da mushirikan Larabawa, ba su zamanto masu barin kafircinsu da suka haɗu a kai ba har sai wata hujja bayyananniya ta zo musu.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wannan hujjar da cewa, wani manzo ne da zai aiko yana karanta musu wasu takardu masu tsarki, watau waɗanda shaiɗanu ba sa iya shafar su sai dai mala’iku masu tsarki. A cikinsu kuma akwai labarai na gaskiya da hukunce-hukunce na adalci waɗanda suke ɗora mutane a kan miƙaƙƙen tafarki na gaskiya.
Wannan shi ne halin da suke ciki kafin aiko Manzon Allah (ﷺ), wai suna dakon zuwan sa, domin ya zo su yi imani da shi. Bayan zuwansa kuma sai suka rarrabu, wasu suka yi imani; wasu kuma suka ci gaba da kafircinsu, suka ƙaryata shi da duk abin da ya zo da shi.
Wannan ya sa Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, Yahudawa da aka ba su littafin Attaura da Nasara da aka ba su littafin Linjila ba su rarraba ba sai bayan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da Annabinsa (ﷺ), daga cikinsu wasu suka musulunta, wasu kuma suka doge a kan kafircinsu, tare da sun tabbatar shi mai gaskiya ne.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna cewa, abin da zai ƙara fito da taurin kan ma’abota littafi a fili shi ne cewa, babu wani umarni da aka yi musu a cikin Alƙur’ani wanda ya saɓa irin umarnin da aka yi musu a littattafansu na cewa, su bauta wa Allah shi kaɗai su guje wa shirka, su kuma tsayar da salla su bayar da zakka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, wannan fa shi ne addinin miƙaƙƙiyar hanya wadda babu karkata a cikinta.
Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan sakamakon waɗanda suka kafirta daga Yahudawa da Nasara da mushirikai, inda ya tabbatar da cewa, za su shiga wutar Jahannama a ranar alƙiyama su kuma dawwama a cikinta har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta ta su da cewa, su ne mafi sharrin halittu, saboda kafircinsu da yadda suka ƙaryata Manzon Allah (ﷺ).
Su kuma waɗanda suka yi imani da Allah da Manzonsa (ﷺ) suka kuma yi ayyuka nagari, to waɗannan su ne mafiya alherin halittu, domin kuwa sakamakonsu a wajen Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, za su shige su su kuma dawwama a cikinsu har abada. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yarda da su saboda sun yi imani da shi sun yi masa ɗa’a, su ma kuma sun yarda da shi saboda cikakkiyar rahamarsa da suka samu. Wannan rahama ta Allah kuwa, sakamako ne ga duk wanda ya ji tsoron sa ya bi umarninsa ya kuma guje wa haninsa.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Duk waɗanda ba su yi imani da manzancin Annabi Muhammadu (ﷺ) ba daga Ma’abota littafi, watau Yahudawa da Nasara, to waɗannan kafirai ne, imaninsu da sauran annabawa da littattafai ba zai amfane su ba.
2. Mushirikai da ma’abota littafi kafin zuwan Manzon Allah (ﷺ) suna rayuwa ne cikin ɓata da ɗimuwa, suna zaton a kan gaskiya suke. To bayan aiko Manzon Allah (ﷺ) sai gaskiya ta bayyana gare su ƙarara, don haka sai wasu suka musulunta suka gaskata Annabi (ﷺ), wasu kuwa sai suka doge a kan ci gaba da zama cikin addinin da suka gada daga iyayensu, duk da cewa sun ga gaskiya ƙuru-ƙuru ta bayyana. Da wannan ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yanke musu hanzari.
3. Muhimmancin ikhlasi wajen bautar Allah, domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ba ya karɓar aikin da babu ikhlasi a cikinsa.
4. Malamai da dama sun kafa hujja da aya ta 5 a kan cewa, ayyuka nagari suna daga cikin imani.
5. Kafirai su ne mafiya sharrin halittun Allah a bayan ƙasa; muminai kuma su ne mafiya alherin halittun Allah kakaf.
6. Tarayyar addinan Allah a kan bauta wa Allah shi kaɗai da bin wasu hukunce-hukuncen shari’a, abu ne da zai sanya dole a yi imani da annabci.
7. Tsoron Allah shi ne babban sanadin shiga Aljanna da samun yardar Allah (Mai tsarki da daukaka).
***