9-Suratut Tauba
Mabuɗin Surar:
1. Sunanta:
Wannan Sura tana daga cikin surori masu sunaye da dama. Daga cikin sunayenta akwai:
- Suratut Tauba. Domin a cikinta an ambaci kalamar ‘tuba’ da yawa. Sannan an yi maganar mutanen nan uku da ba su fita yaƙin Tabuka ba, ba tare da uzuri ba, aka jinkirta tubansu har wani tsawon lokaci kafin Allah ya karɓi tuban nasu daga baya.
- Ana kiran ta da suna ‘Bará’a’ saboda ta buɗe ta da wannan kalma mai nuna barranta daga mushirikai, watau tabbatar da cewa, Allah da Manzonsa ba ruwansu da su.
An karɓo daga Al-Bara’u (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ƙarshen Sura da ta sauka ita ce ‘Suratu Bara’a’.” [Bukhari #4605, da Muslim #1618].
- Ana kiran ta ‘Alfádhiha’:
An karɓo daga Sa’id ɗan Jubairu ya ce: Na tambayi Ibnu Abbas game da Suratut Tauba, sai ya ce: “Tauba ita ce Fádhiha.” [Bukhari #4882, da Muslim#3031].
Fádhiha yana nufin bayyana abin kunyar da wani ya aikata. A cikinta ne Allah ya yi bayanin ababan kunya da munafukai suke aikatawa.
Malamai sun haɗu a kan cewa ba a fara karatun ta da ‘Bisimilla’, saboda sahabbai ba su rubuta ta ba a farkon ‘Mushafin Usman’.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
An saukar da ita a Madina ne. Malamai da yawa sun ambato ijma’i a kan hakan.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Surar ƙarshe da ta sauka a Alƙur’ani. Ita ce Sura ta ɗari da goma sha huɗu (114). Ta sauka bayan ‘Suratul Fat’h’. Malami da dama suna cewa ta sauka ne a dunƙule a lokaci guda.
4. Adadin Ayoyinta:
A lissafin mutanen Makka da Madina da Basra ayoyinta ɗari da talatin ne (130), amma a lissafin mutanen Kufa adadinsu ɗari da ashiri da tara ne (129).
5. Falalarta:
Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) yana cewa: “Ku koyi ‘Suratu Bara’a’, kuma ku koyar da matanku ‘Suratun Nur’.” [Sa’id bn Mansur, Tafsirinsa #1003].
6. Babban Jigonta:
• Tandar wani tsari wanda ya wajaba Musulmi su tafi a kansa wajen alaƙoƙinsu da mushirikai da ma’abota littafi da munafukai.
• Tona asirin munafukai da bayanin siffofinsu da kashe-kahensu da miyagun ayyukansu a cikin al’ummar Musulmi.
• Bayanin hukunce-hukunce masu yawa waɗanda daular Musulunci mai tasowa a wancan lokaci take da buƙata.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Raba gari tsakanin Musulmi da mushirikai da umarnin yaƙar su da watsi da sulhu da aka ƙulla da su da hana su shiga Masallaci mai alfarma.
• Ishara zuwa ga yaƙin Hunaini da darussan da ya ƙunsa game da dogaro da Allah shi kaɗai.
• Shelanta yaƙi da Larabawa ma’abota littafi har sai sun ba da jiziya da bayanin munanan maganunsu game da Uzairu da kuma Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da yadda suke cin dukiyoyin mutane ba da haƙƙi ba.
• Bayani a kan hukuncin watanni huɗu masu alfarma da rushe aƙidar Larabawa ta Jahiliyya game da waɗannan watanni.
• Taimakon Allah ga Annabinsa da babban sahabinsa Abubakar lokacin hijirarsu zuwa Madina da yadda Allah ya kare su daga kafirai.
• Bayanin siffofin munafukai da mugun tanadinsu da ƙulle-ƙullensu a kan Annabi da Musulmi da yawan rantse-rantsen ƙarya da yaɗa ɓarna a cikin al’umma da yi wa raunanan Musulmi izgili da hana nema musu gafarar Allah idan sun mutu da sauran batutuwa da suka dangance su.
• Bayanin falalar sahabban Annabi waɗanda suka fara shiga Musulunci daga cikin masu hijira da mutanen Madina.
• Ambaton ginin Masallacin Ƙuba a bisa ɗa’a ga Allah da taƙawa, kuma shi ne Masallacin da ya kamaci Annabi ya shiga ya yi salla a cikinsa ba masallacin munafukai da suka gina don kawo ruɗani a cikin al’umma da taimaka wa kafirai ba.
• Karɓar tubar wasu sahabbai su uku da suka ƙi halartar yaƙin Tabuka tare da Annabi ba kuma tare da sun gabatar da wani karɓaɓɓen hanzari ba. Allah ya saukar da ayoyin da suka tabbatar an yafe musu laifinsu.
• Kira ga Musulmi a kan neman ilimi na addini da karantar da shi.
• Bayanin baiwar da Allah ya yi wa muminai ta aiko musu da Manzo daga jinsinsu, wanda ya arzuta shi da kyawawan halaye da matuƙar ƙaunar al’ummarsa da tausaya musu.
Da dai sauran batutuwa da Surar ta taɓo bayani a kansu.
1. Allah da Manzonsa ba ruwansu da waɗanda kuka yi alƙawari da su daga cikin mushirikai.
2. To sai ku tafi ku wala a bayan ƙasa tsawon wata huɗu, kuma ku sani cewa ku ba za ku gagari Allah ba, kuma lalle Allah Mai wulaƙanta kafirai ne.
A ayoyi goma sha biyar na farkon wannan Surar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayanin cewa, shi da Manzonsa (ﷺ) ba ruwansu da alƙawarin da yake tsakanin Musulmi da mushirikai na zaman lafiya, sakamakon warware sharuɗɗan zaman lafiya da su mushirikai suka yi. Don haka Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba su tsawon wata huɗu su yi yawo a bayan ƙasa, su je duk inda suke so babu wani Musulmi da zai taɓa su. Lokacin kuma ya fara ne daga ranar sallar layya ta shekara ta tara, ya kuma ƙare a ranar goma ga watan Rabi’ul Akhir a shekara ta goma.
Sai kuma Allah ya ja hankalinsu da cewa, su sani fa ba za su iya gagarar Allah ba, ba za su iya kuɓuce wa uƙubarsa ba idan ya yi nufin kama su. Kuma su sani Allah (Mai tsarki da daukaka) mai wulaƙanta kafirai ne.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Watsi da alƙawarin da ke tsakanin Musulmi da abokan gabarsu yana kasancewa ne a cikin alƙawarin da ba a yanka masa lokaci ba, amma wanda aka riga aka yanka masa lokaci, to za a jira har sai lokacin ya ƙare ko kuma sun warware wani sharaɗi daga cikin sharuɗɗan da aka ambata lokacin ƙulla yarjejeniyar.
2. An ba mushrikai wata huɗu don su sami damar yin tunani a kan al’amarinsu, ko dai su karɓi Musulunci ko kuma su gamu da wulaƙanci na duniya da lahira.
***
