53-Suratun Najm
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da suna ‘Suratun Najm’, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda), ya ce: Annabi (ﷺ) ya karanta ‘Suratun Najmi’ sai ya yi sujjada (watau a ƙarshenta), sai kowa daga cikin mutanensa (Musulmi da mushirikai) suka yi sujjada in ban da mutum ɗaya, shi sai ya cika tafin hannunsa da ƙasa ya kai goshinsa ya ce: “Wannan ya ishe ni.” Abdullahi ya ce: “Na ga wannan mutumin daga baya an kashe shi yana kafiri.” [Bukhari #1070]. Wannan mutumin shi ne Umayyatu ɗan Khalaf.
A wasu littattafan hadisai, kamar Bukhari da Tirmizi an kira ta da suna ‘Suratu Wan-Najmi’, watau kamar yadda lafazin ya zo a cikin Alƙur’ani.
2. Sanda Aka Saukar da Ita:
Sura ce Makkiyya gaba ɗayanta a wurin dukkan malamai.
3. Jerin Saukarta
Ita ce Sura ta ishirin da uku (23) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan 'Suratul Ikhlas' kafin 'Suratu Abasa'.
4. Adadin Ayoyinta:
Malaman Kufa suna ganin ayoyinta sittin da biyu ne (62) amma yawancin masu lissafin ayoyi na sauran garuruwa sun ce sittin da ɗaya ne (61).
5. Babban Jigonta
Tana Magana ne a kan tabbatar da gaskiyar wahayi da bayanin asalinsa mai daraja, domin tabbatar da Tauhidi da rushe shirka.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da gaskiyar Manzon Allah (ﷺ) game da abin da yake isarwa daga Allah da tsarkake shi daga duk wata tuhuma da mushirikai suke yi masa.
• Tabbatar da cewa, Alƙur’ani wahayi ne daga Allah wanda Mala'ika Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo da shi ga Annabi (ﷺ).
• Bayanin siffofin Mala’ika Jibirilu da yadda yake sauka da wahayi.
• Rushe da’awar da mushirikai suke yi ta cewa gumakansu Lata da Uzza da Manata, duk ‘ya’yan Allah ne mata, da tabbatar musu cewa, duk waɗannan gumaka tatsuniyoyi ne ba su da wani tushe ballantana asali.
• Bayanin sakamakon bijirarru da shiryayyu da gargaɗin su a kan su guji maganganu game da gaibu ta hanyar zato kawai ba tare da wata hujja ba.
• Tabbatar da tashi bayan mutuwa.
• Tunatar da su azabar Allah ga al’ummun da suka shuɗe gabaninsu da kuma manzannin da suka zo da shari’u kafin Manzon Allah (ﷺ).
• Tsoratar da su wata azaba wadda take dab da ta auka musu.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Na rantse da tauraro yayin da ya faɗi.
2. Mutumin naku bai ɓata ba, kuma bai kauce hanya ba.
3. Kuma ba ya yin magana bisa son rai.
4. Shi (Alƙur'ani) ba wani abu ne ba in ban da wahayi da ake yiwo (masa).
5. Mai tsananin ƙarfi ne (watau Jibrilu) ya koyar da shi.
6. Mai kyawawan halitta ne, sai ya daidaita.
7. Alhali kuwa shi yana a sassa na can sama.
8. Sannan sai ya kusanto, sai ya ƙara matsawa.
9. Sai ya kasance kamar kusancin kamu biyu ko ƙasa da haka.
10. Sannan (Allah) Ya yiyo wahayin abin da Ya yi wahayi zuwa ga Bawansa (Ma’aiki).
11. Zuciyar (ta Ma’aiki) ba ta yi ƙaryar abin da ta gani ba.
12. Yanzu kwa riƙa jayayya da shi kan abin da yake gani?
13. Haƙiƙa ya gan shi (Jibrilu) a wani karon ma.
14. A wurin Magaryar tuƙewa.
15. A wurinta ne Aljannar makoma take.
16. A yayin da abin da ya lulluɓe Magaryar (na ban mamaki) ya lulluɓe ta.
17. Ganin (nasa) bai karkace ba, kuma bai zarme ba.
18. Haƙiƙa ya ga wasu ayoyin Ubangijinsa manya-manya.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da tauraro yayin da ya faɗi a ƙarshen dare, domin ya tabbatar wa mushirikai cewa mutuminsu, watau Annabi Muhammadu (ﷺ) bai ɓata ya kauce wa hanyar gaskiya ba, bai kuma zama mai sani ya take saninsa ba. Shi mutum ne da yake kan hanyar gaskiya kuma yana aiki da ita. Kuma ba ya magana ta son zuciya. Duk abin da yake karanta musu na Alƙur’ani da wanda yake sanar da su na shari’a ba wani abu ne ba illa wahayi daga Allah, Mala’ika mai tsananin ƙarfi ne ya koyar da shi, watau Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da cewa shi mai kyakkyawar halitta ne, kuma ya daidaita a zahiri a cikin surarsa da Allah ya halicce shi da ita ta mala’ika a lokacin yana can a cikin sassa na sama sosai. Sannan sai ya kusanto Annabi (ﷺ) ya sake matsowa kusa da shi, har sai da kusancinsa da shi ya zamanto kamar kusancin kamu biyu ko ma ƙasa da haka. Sai Jibirilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wahayi zuwa ga bawan Allah Annabi Muhammadu (ﷺ) na abin da ya yi masa wahayi da shi.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, zuciyar Manzon Allah (ﷺ) ba ta yi ƙaryar abin da idanunsa suka gani ba, watau jinsa da ganinsa da zuciyarsa duk sun haɗu a kan tabbatar da abu ɗaya na wahayi da Jibirilu ya yi masa ba su sassaɓa wa juna ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi mushirikai cewa, to yanzu su suna jayayya da Annabi ne (ﷺ) game da abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna masa a daren Isra’i na manya-manyan ayoyinsa?
Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ga Mala’ika Jibirilu a surarsa ta mala'ika da Allah ya halicce shi da ita a wani karo na daban, watau a daren Isra’i a wurin Magaryar tuƙewa, wata bishiya ce babba da ke saman sama ta bakwai, inda duk wani abu da ya hau sama yake tuƙewa.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wurin wannan bishiyar Aljannar makoma take. Kuma wani babban al’amari na Allah ne yake lulluɓe ta wanda babu mai iya siffanta shi sai Allah.
Sai kuma ya bayyana cikar ladabin Manzon Allah (ﷺ) da nutsuwarsa lokacin da Allah ya tsayar da shi wannan matsayi, ganinsa bai karkata dama ko hagu ba, bai kuma ƙetare iyakar da ya shata masa ba.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda), yana cewa: “Manzon Allah (ﷺ) ya ga Ubangijinsa da zuciyarsa sau biyu.” [Muslim #171 da Ahmad #1958].
An karɓo daga Masruƙ ya ce: A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce masa: “Ya kai baban A’isha, duk wanda ya riya cewa Muhammadu ya ga Ubangijinsa, to ya yi wa Allah babbar ƙarya.” Ya ce: Na kasance ina kishingiɗe sai na miƙe zaune na ce: “Ya Uwar Muminai, ki saurara mini kada ki yi mini gaggawa, me za ki ce game da faɗar Allah: “Haƙiƙa ya gan shi a wani karon ma”, da kuma faɗarsa: “Haƙiƙa ya gan shi a sararin (samaniya) mabayyani”? Sai ta ce: “Wannan Jibrilu ne; ya gan shi a wani lokaci a surarsa da aka halicce shi da ita; ya sake ganin sa a wani lokaci na biyu yayin da yake sauka daga sama zuwa ƙasa, girman halittarsa ta cika sama da ƙasa.” Ta ce: “Ni ce farkon wanda na yi wa Manzon Allah (ﷺ) tambaya game da wannan ayar, sai ya ce: “Ai Jibrilu ne.” [Bukhari #3235 da Muslim #177].
An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “An nuna mini Magaryar tuƙewa a sama ta bakwai, ‘ya’yanta kamar kulolin Hajar, ganyenta kuwa kamar kunnuwan giwaye. Daga kututturan itacenta wasu ƙoramu suna fita, biyu a waje, biyu kuma a ciki, sai na ce: “Ya Jibrilu mene ne waɗannan?” Sai ya ce: Ƙoramu biyu na ciki daga Aljanna ne, amma na waje su ne Nilu da Furata.” [Ahmad #12673, Dubi Bukhari #3207 da Muslim #173].
An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Lokacin da na isa wajen Magaryar tuƙewa, sai na ga ganyenta kamar kunnuwan giwaye, ‘ya’yanta kuwa kamar tuluna. Yayin da abin da ya lulluɓe ta daga al’amarin Allah ya lulluɓe ta sai ta rikiɗa ta zama yaƙutu da zumarradu da kwatankwacinsu.” [Ahmad #12301 da Ibn Jarir, Tafsiri, Juzu’i na 22 shafi na 36].
A wata ruwayar ya ce: “Yayin da abin da ya lulluɓe ta na al’amarin Allah ya lulluɓe ta sai ta rikiɗa, babu wanda zai iya siffanta ta saboda kyanta.” [Muslim #162].
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, a daren Mi’iraji Annabi Muhammadu (ﷺ) ya ga manya-manyan ayoyin Ubangijinsa masu nuna cikar Ƙudurarsa, ya ga Aljanna ya kuma ga wuta da abubuwan ban mamaki da dama.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Alaƙar rantsuwar Allah da tauraro a nan shi ne, akwai babbar alaƙa tsakanin taurari masu haskaka sararin samaniya da kuma wahayin da Manzon Allah (ﷺ) ya zo da shi yana karanta wa mutane. Kamar yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanya taurari suka zama ado a sararin samaniya, to hakanan shi ma wahayi yake ado ne ga ƙasa. Ba domin ilimin da annabawa suke bari gado ba, to da mutane sun rayu cikin duhu ƙirin wanda ya fi na dare mai tsananin duhu.
2. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta Annabi (ﷺ) da cewa shi mutumin mutanen Makka ne, domin ya nuna musu cewa, ai sun san shi sarai, sun kuma san tasowarsa ciki da waje tun bai zama Annabi ba, sun san shi mutum ne mai gaskiya da riƙon amana da nutsuwa, to amma sai ga shi yanzu don ya zo yana faɗa musu gaskiya sun kira shi da marar hankali. Wannan babu shakka son zuciya ne ƙarara.
3. Tabbatar da dalili a kan cewa sunnar Annabi (ﷺ) ita ma wahayi ce daga Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma shi Annabi (ﷺ) ma’asumi ne game da duk wani abu da yake isarwa na shari’a, domin ba ya maganar son zuciya sai abin da ake yi masa wahayi da shi.
4. Falalar Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), domin Allah (Mai tsarki da daukaka) ya keɓance shi don ya zama malami ga Annabi (ﷺ) yana karanta masa Alƙur’ani, don haka shi malamin Annabi Muhammadu ne.
5. Ba da kariya ga wahayi, watau Alƙur’ani da tsare shi daga shaiɗanu ta yadda ba za su iya jirkita shi ba ko su su jefa ɓarnarsu a cikinsa, domin wanda yake zuwa da shi mai tsananin ƙarfi ne, watau babu wani shaiɗani da zai iya kusantar sa ballantana ya lalata masa aikensa.
6. Mala’iku halittu ne masu kyan sura masu tsananin ƙarfi.
7. Annabi (ﷺ) ya ga Jibrilu a surarsa wadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halicce shi da ita a daren Mi’iraji.
8. Cikar ladabin Annabi (ﷺ). Ba a taɓa yin mutum mai ladabi a wurin Allah ba tun kafuwar duniya har zuwa tashin alƙiyama kamar Manzon Allah (ﷺ) ba.
9. Tabbatar da cewa, Annabi (ﷺ) ya ga Aljanna da wuta a daren mi’iraji.
***
