46-Suratul Ahƙaf

Mabuɗin Sura:
7. Sunanta:
Ana kiran ta da suna ‘Suratul Ahƙaf’. Hakanan aka ji wannan suna daga wasu sahabbai, kamar Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) da Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda).
An kuma kira ta da wannan suna saboda lafazin Al-Ahƙaf bai zo a wata sura ba sai a cikinta. Al-Ahƙaf sunan wani gari ne a ƙasar Yaman inda Adawa mutanen Annabi Hudu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suka rayu.
8. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Sura ce Makkiyya a wurin dukkan malamai, kamar yadda Ƙurɗubi ya ambata a tafsirinsa. Amma wasu malamai sun keɓe wasu ayoyi huɗu waɗanda suka ce sun sauka ne bayan hijira, watau Madaniyya ne, su ne aya ta 10 da aya ta 15 zuwa ta 18 da kuma aya ta 35.
9. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta sittin da biyar (65) a jerin saukar surorin Alƙur’ani. Ta sauka bayan ‘Suratul Jasiya’ kafin ‘Suratuz Zariyat’.
10. Adadin ayoyinta:
Ayoyinta talatin da biyar ne (35) a lissafin mutanen Kufa, amma a lissafin malaman sauran garuruwa ayoyinta talatin da huɗu ne (34).
11. Babban Jigonta:
Surar tana magana ne a kan tabbatar da Kaɗaitakar Allah da manzancin Annabi (ﷺ) da kuma tabbatar da tashi bayan mutuwa domin yin hisabi da sakamako.
12. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Bayanin matsayin Alƙur’ani da mu’ujizarsa.
• Tabbatar da Kaɗaitakar Allah ta hanyar kafa hujja da halittar sammai da ƙasa da kuma tabbatar da sakamakon ayyuka a ranar lahira.
• Rushe bautar duk wani abin bauta ba Allah ba da nuna rashin cancantar a bauta masa ko a sanya shi abokin tarayya da Allah (Mai tsarki da daukaka).
• Rushe da’awar cewa Alƙur’ani maganar wani ne ba Allah ba.
• Tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu (ﷺ) da kafa shaida a kan haka da mai shaida daga Banu Isra’ila.
• Yabon waɗanda suka yi imani da Alƙur’ani da ambaton wasu kyawawan siffofinsu tare da tsokaci a kan wasu halaye na kafirai, kamar hassada wadda ta sanya su ƙaryata Annabi (ﷺ).
• Labarin wata mu’ujiza ta Manzon Allah (ﷺ), watau zuwan aljannu wurinsa da sauraron karatunsa na Alƙur’ani da yin imani da shi.
• A cikinta an kawo maganar kyautata wa iyaye da kyakkyawar addu’a gare su da kuma ‘ya’ya.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
حمٓ ١ تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ ٢ مَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَمَّآ أُنذِرُواْ مُعۡرِضُونَ ٣ قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ٤ وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ ٥ وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ ٦
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ha Mim.
2. Saukar da Alƙur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.
3. Ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu ba sai don gaskiya da kuma (zuwa) wani lokaci ƙayyadajje. Waɗanda kuwa suka kafirta masu bijire wa abin da aka yi musu gargaɗi da shi ne.
4. Ka ce: “Shin kun ga abin da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta na ƙasa, ko kuwa suna da tarayya ne a (halittar) sammai; ku kawo mini wani littafi da yake gabanin wannan (Alƙur’anin), ko kuma wani ɓirɓishi na ilimi idan kun kasance masu gaskiya.”
5. Wane ne ya fi ɓata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alƙiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?
6. Idan kuma aka tashi mutane (ababen bautar) za su kasance abokan gabarsu, kuma su zamo masu musanta bautar tasu.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta da irin waɗannan haruffa. [Dubi tafsirinmu na farkon Suratul Baƙara domin ƙarin bayani].
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi wannan Alƙur’ani da cewa, saukakke ne daga wajen Allah Mabuwayi wanda babu mai iya rinjayar sa, mai hikima a cikin halittarsa da shari’arsa da tsarinsa.
Sai kuma ya bayyana cewa, bai halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu don wasa ba, ya halicce su ne don gaskiya da wata babbar hikima wadda ta ƙunshi nuna wa bayinsa girman Ƙudurarsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai ba tare da yi masa shirka ba, sannan kuma mutane su rayu a bayan ƙasa da kyakkyawar zamantakewa da khilafa har zuwa wani ƙayyadajjen lokaci da Allah ne kaɗai ya san shi. To amma duk da wannan kafirai ba su daina bijire wa abin da ake musu gargaɗi da shi ba a cikin littafin Allah suna watsi da shi suna bin son zuciyarsu.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya tambayi mushirkai masu bauta wa gumaka ba Allah ba su faɗa masa, wane abu ne suka halitta a bayan ƙasa, shin sun halicci wani dutse ne ko kuma sun halicci wata ƙorama? Ko kuma sun yi tarayya da Allah ne wajen halittar sammai don haka suna da wani kaso a ciki? Ya neme su da su zo masa da wani littafi da Allah ya saukar musu kafin Alƙur’ani ko wani ɓurɓushin ilimi na mutanen farko da ke nuna cewa gumakan da suke bauta wa sun cancanci a bauta musu. Babu shakka ba za su sami wannan ba, saboda haka suna jayayya ne kawai ba da wata hujja ba ta ilimi ko ta hankali.
Sannan Allah ya bayyana wautarsu a fili yayin da suke bauta wa gunki wanda ba zai taɓa amsa addu’ar ɗayansu ba har alƙiyama ta tashi, hasali ma su waɗannan gumakan da suke bauta wa ba su ma san suna yi ba ballantana har su amsa musu addu’o’insu, ko su amfanar da su ko su kare musu wata cuta. Don haka babu ɓatacce kamar mai bautar wani ba Allah ba.
Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana rashin amfanin bautar wani ba Allah ba a ranar alƙiyama, lokacin da za a tattara su gaba ɗayansu domin yi musu hisabi, to a lokacin ababen bautarsu ba Allah ba za su zame musu abokan gaba, su riƙa nesanta kansu da su, har su nuna musu cewa, su ba su san da bautar da suka yi musu ba a duniya.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Bayani a kan girman Alƙur’ani da babban matsayinsa don bayin Allah su haskaka da haskensa su yi riƙo da shiriyarsa.
2. Babbar manufar halittar sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu, don su zama ƙaƙƙarfar hujja da ke nuna Ɗayantakar Allah da kuma cancantar a bauta masa shi kaɗai, don kuma bayi su yi kyakkyawan tanadi na zuwan ranar alƙiyama da abin da ta ƙunsa na hisabi da sakamako.
3. Kafirai sun bijire wa tuntuntuni game da halittar sammai da ƙasa, waɗanda suke nuna Kaɗaitakar Allah da cikar Ƙudurarsa.
4. Dukkan abin da aka bauta wa ba Allah ba to kasasshe ne bai cancanci bauta ba. Allah ne kaɗai ya cancanci bauta domin shi ne mahaliccin sammai da ƙasa da abin da yake cikinsu.
5. Babu wani bayani ɗaya da za a samu daga wani manzo daga cikin manzannin Allah da yake nuna a bauta wa wani ba Allah ba. Duk annabawan Allah sun yi kira ne zuwa ga kaɗaita Allah da bauta da guje wa shirka.
6. Amsa addu’a tana daga cikin fitattun dalilai masu nuna samuwar Allah da cancantar a bauta masa shi kaɗai.
7. Duk waɗanda suka bauta wa wasu ba Allah ba, to a ranar alƙiyama sai sun yi baram-baram da su su nesanta kawunansu daga bautarsu.