113-Suratul Falaƙ

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura ta shahara da suna ‘Suratul Falaƙ’, saboda kalmar ‘Al-Falaƙ’ da ta zo a ayarta ta farko. Amma a mafi yawan hadisai da maganganun sahabbai an kira ta da ‘Suratu Ƙul A’uzu Bi Rabbil Falaƙ’.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Sura ce Makkiyya bisa magana mafi inganci.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta ashirin (20) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratul Fili’ kafin ‘Suratun Nasi’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta biyar ne (5).
5. Falalarta:
Hadisai da yawa sun inganta game da falalarta tare da ‘Suratun Nas’ da ‘Suratul Ikhlas’; daga cikinsu akwai:
• Hadisin A’isha (Allah ya kara mata yarda) inda ta ce: Annabi (ﷺ) ya kasance a duk dare idan ya zo kwanciya sai ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya yi tofi a cikinsu, sai ya karanta ‘Ƙul Huwallahu Ahad’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbil Falaƙ’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbin Nasi’ sannan ya shafe jikinsa gwargwadon ikonsa da su; yana farawa ta kansa da fuskarsa da gaban jikinsa, yana yin haka har sau uku. [Bukhari #5017 da Abu Dawud #5056 da Tirmizi #3399].
• An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Kunama ta harbi Manzon Allah (ﷺ) yana cikin salla, yayin da ya gama sai ya ce: “Allah ya la’anci kunama, ba ta ƙyale mai salla ba balle waninsa.” Sai ya nemi a kawo masa ruwa da gishiri, sai ya riƙa shafa su a wurin harbin yana karanta ‘Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbil Falaƙ’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbin Nas’. [Ɗabarani, Al-Mu’ujamus Saghir, shafi na 117. Dubi, Al-Albani, As-Sahiha #548].
• An karɓo daga Uƙuba ɗan Amir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya Uƙubatu ɗan Amir, yanzu ba na sanar da kai wasu surori waɗanda ba a saukar da kamarsu ba a cikin Attaura da Linjila da Alƙur’ani? Kada ka bari wani dare ya wuce ka sai ka karanta su a cikinsa, su ne, ‘Ƙul Huwallahu Ahad’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbil Falaƙ’ da ‘Ƙul A’uzu Bi Rabbin Nas’.” [Ahmad #17452].
6. Dalilin Saukarta:
Zaidu ɗan Arƙam (Allah ya kara masa yarda) ya ruwaito cewa, akwai wani Bayahude da yake zaune wajen Annabi (ﷺ), yana shiga har cikin gidansa, (wato kafin a saukar da ayar hijabi). Annabi (ﷺ) ya amince masa, to amma sai ya yi wa Manzon Allah wasu ƙulle-ƙullen sihiri ya jefa a cikin rijiyar wani mutumin Madina, sai Manzon Allah (ﷺ) ya kamu da rashin lafiya na tsawon wata shida. Sai wasu mala’iku biyu suka zo duba shi, ɗaya ya zauna a daidai kansa, ɗayan kuma ya zauna a daidai ƙafafunsa. Sai ɗaya ya tambayi ɗan’uwansa: "Ka san mene ne rashin lafiyarsa?" Sai ya amsa masa cewa: "Ai mutumin nan 'wane' ne da yake zuwa wajensa shi ne ya yi masa wasu ƙulle-ƙulle, ya jefa a cikin rijiyar 'wane' mutumin Madina. Da a ce zai aika wani zuwa wannan rijiya don ya samo ƙulle-ƙullen, da zai ga ruwan rijiyar ya yi fatsi-fatsi. Sai Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo masa da ƙula'uzai biyu, ya faɗa masa cewa: " 'Wane' Bayahude, shi ne ya yi maka sihiri, sihirin kuma yana can cikin rijiyar 'wane'". Sai Manzon Allah (ﷺ) ya tura Aliyyu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da ya je ya sami ruwan wannan rijiya ya yi fatsi-fatsi, ya kuma ciro waɗannan ƙulle-ƙulle ya kawo wa Manzon Allah (ﷺ), sai Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya umarce shi ya kwance ƙulli ɗaya ya karanta aya ɗaya. Yana yi sai ya fara jin sauƙi. Duk sanda ya kwance ƙulli ya karanta aya ɗaya sai ya ƙara jin sauƙin yana ƙaruwa, haka ya yi ta kwance su ƙulli-ƙulli yana karanta musu aya ɗaya-ɗaya, yana gamawa sai ya ji ya warke gaba ɗaya, ya miƙe cikin nishaɗi kamar ba abin da ya taɓa samun sa. [Dubi, Ɗabarani, Al-Mu’ujamul Kabir #5011 da 5013 da 5016 da Ahmad #19267 da Nasa’i #4080].
7. Babban Jigonta:
Tana umarni da neman tsarin Allah (Mai tsarki da daukaka) daga duk wani sharri na sarari da na ɓoye.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ ١ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ ٢ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ ٣ وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَٰتِ فِي ٱلۡعُقَدِ ٤ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ ٥
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin asuba.
2. “Daga sharrin abin da Ya halitta.
3. “Da kuma sharrin dare idan ya lulluɓe da duhu.
4. “Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle.
5. “Da kuma sharrin mai hassada yayin da ya yi hassadar.”

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) da ya nemi tsari da kariyar Ubangijin asuba daga sharrin duk wani mahaluƙi mai cutarwa, mutum ne ko aljani ko dabba. Ya kuma nemi tsarinsa daga sharrin duk wani abu da sharrinsa yake bayyana a cikin dare yayin da ya lulluɓe da duhunsa, kamar wasu miyagun dabbobi ko ƙwari ko ɓarayi. Ya kuma nemi tsari daga sharrin mata masu sihiri waɗanda suke tofi a cikin ƙulle-ƙullensu na sihiri. Ya kuma nemi tsarinsa daga duk wani mahassadi idan ya yi aiki da abin da hassadarsa ke saƙa masa.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Gaskiyar sihiri da hanyar magance shi.
2. Yawancin masu niyyar aikata sharri, suna fitowa ne da daddare domin ƙoƙarin ɓoye kansu.
3. Masu sihiri babban sharri ne a cikin al’umma, don haka Musulunci ya yi umarni da a kashe su.
4. Hassada babbar cuta ce mai kama zuciya wadda take sa mutum ya riƙa fatan gushewar wata ni’ima daga ɗan’uwansa, don haka zai yi ta ƙoƙari don ganin ya cim ma mummunan burinsa.
5. Surar ta ƙunshi neman tsari daga dukkan nau’o’in sharri baki ɗaya.

***