1-Suratul Fatiha

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran wannan Sura da suna ‘Fatihatul Kitab’, kamar yadda ya zo cikin hadisin Ubadatu ɗan Samit (Allah ya kara masa yarda) [Dubi, Bukhari #756 da Muslim #394], saboda ita ce Sura ta farkon a cikin Alƙur'ani.
Hakanan ana kiran ta da sunaye kamar: Ummul Ƙur'an [Dubi, Bukhari #772, da Muslim #772]. Ana kiran ta Ummul Kitab da Sab'ul Mathani, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Abu Huraira [Abu Dawud #1457 da Tirmizi #3124].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
An saukar da ita a Makka bisa ga ra'ayin da dama daga cikin malamai.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta biyar (5) a jerin saukar surorin Alƙur'ani.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta bakwai ne (7), bisa ga ra'ayin mafiya yawan malamai.
5. Falalarta:
Hadisai sun zo da bayanin falalar karanta ta:
• Dole ne mutum ya karanta ta a cikin sallolinsa, idan bai karanta ta ba to ba shi da salla. [Dubi, Bukhari #756 da Muslim #394].
• Ita ce mafi girman Sura da aka saukar a cikin Alƙur'ani da Attaura da Injila. [Dubi, Bukhari #4474].
• Ita ce surar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya raba ayoyinta tsakaninsa da bawansa mai karanta ta, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda). [Muslim #395].
• Ita ce ruƙya da ake karanta ta don neman waraka daga wata rashin lafiya, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu Sa'id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda). [Bukhari #5007 da Muslim #2201].
6. Babban Jigonta:
Tabbatar da wajabcin fuskantar da bauta ga Allah shi kaɗai.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Surar ta ƙunshi ishara zuwa ga abin da Alƙur'ani ya ƙunsa na bayanin kaɗaitar Allah Ta'ala da siffofinsa da cancantar a bauta masa shi kaɗai.
• Kamar yadda ta ƙunshi ishara zuwa ga tabbatar da tashin alƙiyama wanda Allah zai yi hisabi a cikinsa ya saka wa kowa gwargwadon aikinsa.
• Kamar yadda ta nuna karkasuwar mutane zuwa gida uku: Kaso na farko su ne waɗanda suka san gaskiya kuma suka yi aiki da ita. Waɗannan su ne masu samun babban rabo. Sai kaso na biyu, waɗanda suka san gaskiya sannan suka bijire mata. Waɗannan su ne waɗanda Allah ya yi fushi da su. Sai kaso na uku, su ne waɗanda suke aikin ɓata cikin jahilci da ɗimuwa. Waɗannan su ne ɓatattu.
• Surar tana yin ishara da wannan ne zuwa ga abin da Alƙur'ani ya ƙunsa na tarihin al'ummomi da kashe-kashensu.

***


بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ١
【Tarjama】

1. Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai

【Tafsiri】

Malamai sun haɗu a kan cewa, Bisimilla Alƙur'ani ce, kuma aya ce a cikin ‘Suratun Namli’; sai dai sun saɓa a kan cewa, shin aya ce a farkon kowace sura ko a'a? Zance dai mafi rinjaye shi ne ita aya ce a farkon ‘Suratul Fatiha’, sannan an saukar da ita a farkon kowace sura don bambance tsakanin ƙarshen sura da farkon wata sura. Amma ban da tsakanin ‘Suratul Anfal’ da ‘Taubah’.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Alƙur’ani da ambaton sunansa Allah, wato sunan da ya cancanta a bauta masa shi kaɗai da shi, saboda ya siffantu da siffofin kamala. Daga cikinsu akwai siffofinsa kuma sunayensa: Arrahman wanda yake nuna yalwatacciyar rahmar Allah wadda take shafar kowa da komai a nan duniya da kuma sunansa Arrahim, wanda suke nuna keɓantacciyar rahamarsa a lahira ga muminai kawai masu tsoran sa. Don haka wajibi ne mumini ya tabbatar wa Allah dukkan sunayensa da siffofinsa kamar yadda suka zo a Alƙur'ani da sunnar Annabi (ﷺ) ba tare da canza musu ma'ana ba, ko kamanta su da siffofin halittarsa ba.

***