إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ ٥
【Tarjama】

5. Kai kaɗai muke bautata wa, kuma Kai kaɗai muke neman taimakonka.

【Tafsiri】

Watau Allah kaɗai muka yarda mu bauta wa; dukkan nau'o'in ibada gare shi ake ba da su. Ibada kuwa ita ce, duk wani abu da Allah yake son sa kuma ya yarda da shi, na ƙuduri ne a zuciya ko magana ta baka ko kuma aiki na gaɓobi. Sannan mun tabbata ba za mu iya bauta masa yadda ya dace ba sai da taimakonsa. Don haka a wajensa kaɗai muke neman taimako a cikin lamuranmu gaba ɗaya. Wannan yana nuna ba a neman taimakon wani wanda ba Allah ba a duk wani abu da Allah ne kaɗai zai iya yin sa, kamar bayar da arziki ko neman lafiya ko neman 'ya'ya da makamantansu. Bai halatta wani ya kira wani annabi ko wani waliyyi ko wani salihin bawa ba yayin da yake cikin wata musiba don ya taimake shi, idan har ya yi haka to ya bayar da haƙƙin Allah ga wani, watau ya yi shirka da Allah.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga wannan ayar za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Wajabcin tsantsanta bauta ga Allah (Mai tsarki da daukaka) da kuma neman cikakken taimako wajensa shi kaɗai.
2. Nisantar shirka kowace iri ce.
3. Bawa ya dogara ga Allah shi kaɗai ya nemi taikmakonsa a kan dukkan al'amurarsa. Hatta bautar Allah (Mai tsarki da daukaka) ba za ta yiwu ba ga bawa har sai Allah ya dafa masa.