27. Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku ha’inci Allah da Manzo, (kada) kuma ku ha’inci amanoninku alhali kuna sane.
28. Kuma ku sani cewa, dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne, Allah kuma lalle a wurinsa lada mai girma yake.
29. Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kuka kiyaye dokokin Allah, to zai sanya muku (hanyar) tsira Ya kuma kankare muku munanan ayyukanku kuma Ya gafarta muku. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne.
A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana umartar muminai da su nesanci cin amanarsa da ta Manzonsa (ﷺ) da kuma duk wata amana da suka danƙa a tsakaninsu alhalin suna sane.
Amanar Allah ita ce bin dokokinsa ta hanyar aikata duk wani wajibi da barin duk wani abin da aka hana. Kiyaye amanar Manzon Allah (ﷺ) kuwa shi ne yi masa biyayya da girmama sunnarsa da aiki da ita.
An karɓo daga Abu Hurairata (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah ya ce: “Alamomin munafuƙi uku ne: Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya, idan kuma aka yi alƙawari da shi sai ya saɓa, kuma idan an amince da shi sai ya ci amana.” [Bukhari #33, da Muslim #59].
Sannan kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗakar da muminai cewa, dukiyarsu da ‘ya’yansu wata jarraba ce daga Allah gare su, domin ya ga shin za su bayar da haƙƙin Allah da ke cikinsu ko kuma son zuciya zai rufe musu ido su fifita son dukiyoyinsu da ‘ya’yansu a kan son Allah. Kuma ya kwaɗaitar da su cewa, duk wanda ya yi biyayya ga umarninsa yana da wani lada mai girma a wurinsa. Kuma idan har sun kiyaye dokokin Allah, sun bi umarninsa, sun guji haninsa, to zai sanya musu wata alama da za su bambance tsakanin ƙarya da gaskiya da ita, ya kuma sanya musu mafita daga duk wata damuwa ta duniya, ya ba su nasara, ya ƙarfafe su, kuma zai kankare musu laifukansu ya yafe musu. Allah kuwa ma’abocin babbar falala ne.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Haramcin cin amana komai ƙarancinta.
2. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana jarrabar bayinsa da ni’imomin da ya ba su na dukiya da ‘ya’ya.
3. Jin daɗin lahira shi ne mafi girman jin daɗi wanda ba ya yankewa.
4. Tsoron Allah ga bawa shi ne alamar rabautarsa duniya da lahira.
5. Duk mai tsoron Allah, Allah zai ba shi damar bambance tsakanin gaskiya da ƙarya.
6. Tsoron Allah, wato kiyaye dokokinsa, ita ce hanyar kuɓuta daga duk wata damuwa ta duniya da ta lahira.
***
