159. To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai ƙeƙasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka ƙulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi.
160. Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya taɓar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kaɗai.
161. Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha’inci. Duk wanda ya yi ha’inci kuwa zai zo da abin da ya ha’inta ranar tashin alƙiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba.
A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) yana faɗa wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai sauƙin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu’amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi.
An karɓo daga Aɗa’u ɗan Yasar ya ce: “Na gamu da Abdullahi da Amru ɗan Asi (Allah ya kara masa yarda), sai na ce masa: “Faɗa mini siffar Annabi (ﷺ) da take cikin littafin Attaura.” Sai ya ce: “Ƙwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alƙur’ani, inda Allah yake cewa: “Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargaɗi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna ‘Mai dogaro’, ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa, ya yi gafara. Kuma Allah ba zai karɓi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta buɗe idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe.” [Bukhari #2124].
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da ya yi afuwa a kan kurakuransu da gajiyawarsu, kuma ya nema musu gafarar Allah (Mai tsarki da daukaka), ya kuma nemi shawararsu cikin abubuwan da kan taso masu buƙatar sai an yi shawara. Bayan shawara kuma, duk abin da ya ga shi ne ya fi maslaha, to ya ci gaba da zartar da shi, ya dogara ga Allah, Allah yana son masu dogara da shi.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa muminai cewa, idan har ya ƙaddara musu samun wata nasara, to babu wanda ya isa ya karya su ko ya ci galaba a kansu; idan kuwa ya yi watsi da su, ya ƙyale su, to har abada babu mai iya taimakon su, don haka lalle muminai su dogara da Allah shi kaɗai.
Sannan Allah ya faɗakar da cewa, ba ya daga cikin halayen annabawa su saci dukiyar ganima, domin Allah ya tsare su daga cin amana ko wani mugun hali, don haka bai dace a tuhume su da wani abu irin wannan ba.
Yawancin makaranta sun karanta ayar kamar haka: (أنْ يُغَلّ) watau suka yi rufu’a a kan (يُـ), suka kuma yi fataha a kan غَـ)). Ma’ana: “Bai kamata ba a ha’inci wani annabi.…”
Sai kuma ya ambaci sakamakon wanda ya saci dukiyar ganima da cewa, zai zo ɗauke da kayanta a ranar gobe ƙiyama a gadon bayansa, sannan kowane rai za a yi masa sakayya a kan aikinsa, kuma babu wanda za a zalunta komai.
An karɓo daga Mu’azu ɗan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya aike ni, bayan na kama hanya na tafi, sai kuma ya aika a kirawo ni. Da na dawo sai ya ce: “Ko ka san don me na aika a kirawo ka? Kada ka kuskura ka ɗauki wani abu na ganima ba tare da izinina ba, domin yin haka satar dukiyar ganima ce wanda duk ya saci dukiyar ganima, to zai zo da abin da ya sata ranar alƙiyama. Don haka ne na kirawo ka, sai ka tafi wurin aikinka.” [Bukhari #200].
An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Ranar yaƙin Khaibara, wasu sahabbai sun zo suna lissafa wa Manzon Allah (ﷺ) cewa, wane ya yi shahada, wane ma ya yi shahada, har suka zo kan wani mutum, sai suka ce, wane ma ya yi shahada.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A’a, ba haka ba ne, ni na gan shi a wutar Jahannama saboda wani mayafi da ya sata daga dukiyar ganima.” Sannan Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya kai ɗan Khaɗɗab, tafi ka yi shela a cikin mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai muminai kaɗai.” Ya ce: “Sai na fita na shelanta wa mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai mumini kaɗai.” [Muslim #114].
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Kwaɗaitarwa a kan kyawawan halaye da tausasawa wajen mu’amala, domin yin haka ne yake kawo haɗin kai na al’umma, ya haifar da soyayyar juna; rashinsa kuma shi ne yake haifar da rarrabuwar kai da ƙiyayyar juna.
2. Kyawawan halayen shugaba na addini sukan sa mutane su gane addinin, su karɓe shi, yayin da miyagun halayensa kan iya sa mutane su nisanci addinin, su tsane shi.
3. Neman shawara ibada ce da mai yin ta zai sami kusanci ga Allah.
4. A cikin neman shawara akwai hikimomi da yawa, daga cikinsu akwai:
• Hana shugaba yin mulkin kama-karya.
• Koya wa mutane yaddda za su gudanar da al’amuransu, su sami gogewa a kai.
• Koyar da tawali’u wajen neman shawara. Domin duk shugaban da yake neman shawara a kan lamuransa, wannan yana nuna shi mai tawali’u ne.
• Motsa kuzarin al’umma. Yayin da za su ga ana neman shawararsu wannan zai ƙara musu kuzari a kan ayyukan alheri.
• Idan ra’ayoyi daban-daban suka haɗu tare da kyakkyawar niyya, sau tari akan dace da daidai. Domin mutum shi kaɗai zai iya hango maslahar wani al’amari, amma ya kasa gano ɓarnar da ke cikinsa, musamman ma idan idonsa ya rufe wajen son wannan abu; to amma bayan an yi shawara sai a gane duk abin da ke ciki na maslaha da na ɓarna.
• Idan an gudanar da kowane abu ta hanyar shawara, to ba za a sami rarrabuwar jama’a ba, domin karɓaɓɓun mutane masu gaskiya da gogewa a cikin al’amura, su ne ake neman shawararsu.
5. Haramun ne wani ya ci amanar wani, ko ya saci dukiyarsa. Keɓance Annabi (ﷺ) da ambato a ƙira’ar da aka ce: “Bai kamata ba a ci amanar wani annabi…”, yana nuna duk sanda wanda aka yi wa laifin ya zamanto babban mutum ne mai daraja, to laifin ya fi girma da tsanani. Manzon Allah (ﷺ) shi ne mafificin halitta, don haka yi masa laifi ya fi tsanani da muni. Sannan kuma shi Annabi (ﷺ) ana yi masa wahayi lokaci bayan lokaci, don haka duk wanda ya ha’ince shi, to wahayi na iya sauka nan take ya tona asirin mai ha’incin tun a duniya, baya ga azabar lahira idan ya mutu bai tuba ba. Sannan kuma Musulmi a lokacin suna cikin matsanancin talauci, don haka ha’inci a sannan yake da matuƙar muni.
6. Dogaro ga Allah yana nufin mutum ya riƙe sabubba tare da mayar da al’amarinsa ga Allah.
7. Idan mutum ya bi dukkan hanyoyi da suka cancanta wajen neman wani abu ko aikata wani abu, sannan ya nemi taimakon Allah ta hanyar dogaro gare shi, to kada ya tsaya kai-komo wajen zartar da abin da ya yi ƙuduri, ta yadda al’amarinsa zai zamar masa damuwa da rashin kwanciyar hankali.
***