99-Suratuz Zalzala

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Yawancin magabata sun kira ta da ‘Suratu Iza Zulzilat’.
An karɓo daga Mu’azu ɗan Abdullahi Al-Juhani (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji wani mutum ɗan ƙabilar Juhaina yana cewa: “Ya ji Manzon Allah (ﷺ) yana karanta ‘Iza Zulzilatil Ardhu’ a sallar asuba, a duka raka’o’inta biyu.
A cikin wasu tafsirai an kira ta ‘Suratuz Zilzaal’.
Muƙatil ɗan Sulaiman ya kira ta ‘Suratuz Zalzala’ kamar yadda yake a cikin Mus'hafin da ke hannuwanmu.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna ganin Sura ce Madaniyya.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta tis’in da huɗu (94) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratun Nisa’i’ kafin ‘Suratul Hadid’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta takwas ne (8) a wurin mutanen Kufa. Amma a wurin yawancin malamai lissafin ayoyi, ayoyinta tara ne (9).
5. Babban Jigonta:
Tana tabbatar da zuwan alƙiyama da hisabin ayyukan bayi masu kyau da munana.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da tashin alƙiyama da aukuwar wasu alamominta da firgitar mutane yayin faruwansu.
• Fitowar mutane domin gudanar da hisabin ayyukansu masu kyau da munana, manya da ƙanana.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا ١ وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا ٢ وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا ٣ يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا ٤ بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا ٥ يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ ٦ فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ ٧ وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ ٨
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Idan aka girgiza ƙasa matuƙar girgiza ta.
2. Ƙasar kuma ta fitar da nauyaye-nauyayenta.
3. Mutum kuma ya ce: “Me ya same ta?”
4. A wannan ranar ne za ta ba da labaranta.
5. Don Ubangijinka Ya umarce ta (da yin haka).
6. A wannan ranar mutane za su fito a warwatse, don a nuna musu ayyukansu.
7. To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi.
8. Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da ba da labarin lokacin tashin alƙiyama, watau yayin da ƙasa za ta yi matuƙar girgiza ta fitar da matattun da suke cikinta da sauran ma’adanan ƙarƙashinta. A lokacin mutum zai ɗimauce ya riƙa cewa, me ya same ta ne take wannan girgiza mai tsanani?
An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ƙasa za ta amayo ‘ya’yan cikinta (manya-manya) kamar dirkoki na zinari da azurfa, sai wanda ya yi kisa ya zo ya ce: ‘A kan wannan ne na yi kisa’; sai mai yanke zumunci ya zo yana cewa: ‘A kan wannan ne na yanke zumuncina’; sai ɓarawo shi ma ya zo ya ce: ‘A kan wannan ne aka yanke mini hannuna’. Sannan sai su duka su bar wannan dukiya ba tare da sun ɗauki komai daga cikinta ba.” [Muslim #1013 da Tirmizi #2208].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan rana ce ƙasa za ta ba da labaran ayyukan da aka aikata a kanta na alheri ko na sharri, domin Allah Ubangijinta ya umarce ta da yin haka, don haka ba za ta saɓa umarninsa ba.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a wannan rana ce mai tsanani da abin tsoro, mutane za su fito zuwa wurin hisabi ƙungiya-ƙungiya, domin a nuna musu ayyukansu masu kyau da munana, waɗanda suka aikata a duniya.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana sakamakon kowa da cewa, duk wanda ya yi wani aikin alheri gwargwadon 'zarra', watau daidai da nauyin jaririyar tururuwa, to zai ga aikinsa a gabansa. Hakanan duk wanda ya yi wani aikin sharri gwargwadon 'zarra', watau daidai da nauyin jaririyar tururuwa, to zai gan shi a gabansa.
An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: An tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: Ya Manzon Allah, mene ne hukuncin zakkar jakai? Sai ya ce: “Ba a saukar mini da komai ba dangane da jakai, sai wannan gamammiyar ayar cewa: “Wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi. Wanda kuma duk ya yi aikin sharri daidai da zarra zai gan shi.” [Bukhari #2371 da Muslim #987].

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Rikirkicewar tsarin gudanar duniya yayin tsayuwar alƙiyama.
2. Ɗimaucewar kafiri lokacin da zai ga wasu abubuwan ban tsoro suna ta faruwa ba zato ba tsammani.
3. Ƙasa za ta ba da shaida a kan ayyukan da mutane suka aikata a kanta.
4. Kwaɗaitarwa a kan aikin alheri komai ƙanƙantarsa da tsoratarwa game da aikata sharri komai ƙanƙantarsa.