97-Suratul Ƙadr
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura an fi sanin ta da ‘Suratul Ƙadr’. Amma wasu magabata suna kiran ta da ‘Suratu Inna Anzalnahu’, wasu kuma su ce ‘Suratu Inna Anzalnahu Fi Lailatil Ƙadr’.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna cewa Sura ce Makkiyya, amma akwai ‘yan kaɗan masu ganin Madaniyya ce.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta ashirin da biyar (25) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratu Abasa’ kafin ‘Suratus Shams’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta biyar ne (5) a lissafin mutanen Madina da Basra da Kufa. Amma a wurin mutanen Makka da Sham adadinsu shida ne (6).
5. Babban Jigonta:
Tana bayanin darajar Alƙur’ani mai girma da falalar Lailatul-Ƙadari.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Bayanin falalar Alƙur’ani.
• Mayar da martani ga masu ganin Alƙur’ani ba saukakke ne daga Allah ba.
• Kwarzanta girman darajar lokacin da aka sauko da Alƙur’ani a cikinsa, watau daren Lailatul-Ƙadari, wanda a cikinsa ne mala’iku suke sauka.
• Kwaɗaitar da Musulmi game da neman daren Lailatul-Ƙadari da yin ibada a cikinsa.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Lalle Mu Muka saukar da shi (Alƙur’ani) a daren Lailatul-Ƙadari (dare mai daraja).
2. Mene ne ya sanar da kai mece ce Lailatul-Ƙadari?
3. (Daren) Lailatul-Ƙadari ya fi wata dubu alheri.
4. Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu.
5. Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tabbatar da cewa, ya saukar da Alƙur’ani a daren Lailatul-Ƙadari cikin watan Ramadana, watau ya saukar da jimillarsa a sama ta kusa a cikin wannan daren, kamar yadda a cikinsa ne ya fara saukar da shi ga Manzon Allah (ﷺ) a Kogon Hira.
Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An saukar da Alƙur’ani a dunƙule lokaci guda daga Lauhul Mahfuzu zuwa Baitul-Izza a sama ta kusa, sannan ya sauka ga Annabi (ﷺ) guntu-guntu gwargwadon buƙata a cikin shekara ashirin da uku.” [Al-Hakim #4216, Ibn Abi Shaiba #30190].
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, ko ya san irin yawan albarka da tarin alheri da ya sanya a cikin daren Lailatul-Ƙadari?
Sai ya bayyana masa cewa, wannan dare babban dare ne, domin kuwa ya fi wata dubu alheri, watau ga wanda zai yi sallolin dare a cikinta yana mai neman lada a wurin Allah.
An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: "Duk wanda ya yi tsayuwar dare a cikin Lailatul-Ƙadari yana mai imani da neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa". [Bukhari #1910 da Muslim #760].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, mala’iku tare da Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) suna saukowa a cikinsa da duk wani abu da Allah ya ƙaddara na arziki da mutuwa da haihuwa da duk wani abu da zai faru a wannan shekarar. Suna kuma saukowa ne da izinin Ubangijinsu.
Sannan ya bayyana cewa, shi wannan dare dukkansa mai albarka ne da aminci tun farkonsa har zuwa ƙarshensa, watau lokacin huduwar alfijir.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Na ga dukkan mafarkanku sun haɗu a kan goman ƙarshe, don haka ku nemi wannan dare a cikin kwanaki mara na wannan goman.” [Muslim #1165].
An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku lalubi daren Lailatul-Ƙadari a kwanakin mara na goman ƙarshe na watan Ramadana.” [Bukhari #2017 da Muslim #1169].
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Girman matsayin Alƙur’ani a wurin Allah.
2. Bayanin lokacin da aka fara saukar da Alƙur’ani, watau cikin daren Lailatul-Ƙadari a watan Ramadana.
3. Falalar daren Lailatul-Ƙadari da ɗimbin alherin da yake cikinsa da bayanin cewa, ibada a cikinsa ta fi ibadar wata dubu da babu Lailatul-Ƙadari a cikinsu.
4. Kwaɗaitar da Musulmi a kan ribatar wannan dare da bautar Allah a cikinsa da ɗimbin alherin da bawa zai samu.
5. Bayanin darajar wannan al’umma da yadda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya keɓance su da wannan babbar falala da bai yi wa sauran al’ummu ba.
6. Fifikon Mala’ika Jibrilu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a kan sauran mala’iku.
7. A cikin daren Lailatul-Ƙadari ne Allah (Mai tsarki da daukaka) yake kasafta duk wani abu da zai wakana a shekara. Imani da haka wani sashi ne na imani da Ƙaddara.
***
