96-Suratul Alaƙ

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
A mafi yawan littattafan tafsiri da mus'hafai ana kiran ta ‘Suratul Alaƙ’. Amma ta shahara a zamanin sahabbai da suna ‘Suratu Iƙra’a Bismi Rabbik’.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Ita ce Surar da aka fara saukar wa Manzon Allah (ﷺ).
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta farko, kamar yadda ya tabbata a cikin littattafan hadisai da na sira, kuma wannan ita ce mafi ingancin magana ta malamai.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta goma sha tara ne (19) a lissafin mutanen Kufa da Basra. A wurin mutanen Sham kuwa goma sha takwas ne (18). Amma a lissafin mutanen Madina da Makka adadinsu ashirin ne (20) daidai.
5. Dalilin Saukarta:
A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ruwaito cewa, farkon abin da aka fara nuna wa Manzon Allah (ﷺ) shi ne mafarki, kuma duk sanda ya yi mafarki sai ya gan shi kamar hasken asuba. Sannan aka sanya masa son zama shi kaɗai, domin ya kasance yana fita zuwa kogon wani dutse a Makka da ake kira Dutsen Hira; yakan zauna shi kaɗai a wannan kogo tsawon wasu kwanaki har guzurin da ya fita da shi ya ƙare, sai ya dawo gida wurin Nana Khadija (Allah ya kara mata yarda) don ya sake tanadar wani guzurin. Yana cikin haka wata rana sai kawai Mala’ika Jibrilu ya zo kwatsam ba zato ba tsammani, ya ce wa Manzon Allah (ﷺ): “Yi karatu!” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ai ni ba mai karatu ba ne.” Sai ya kama Annabi (ﷺ) ya matse shi har sai da ya wahala sannan ya sake shi ya ce masa: “Yi karatu!” Sai ya ce: “Ai ni ba mai karatu ba ne.” Sai ya sake kama shi ya matse shi a karo na biyu, sannan ya sake shi ya ce: “Yi karatu!” Sai ya ce: “Ni ba mai karatu ba ne.” Sai ya kama shi ya matse a karo na uku sannan ya sake shi ya ce: “Yi karatu da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta....” har zuwa ƙarshen aya ta 5. [Bukhari #3 da Muslim #160].
6. Babban Jigonta:
Mutum ba ya zama cikakken mutum sai ta hanyar ilimi wanda aka haɗa shi da sunan Allah, mai sanya bawa ƙanƙantar da kai ga Ubangijinsa. Rashin wannan kuwa nakasa ce gare shi.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Koya wa Manzon Allah (ﷺ) karatun Alƙur’ani lokacin da bai san karatu da rubutu ba.
• Nuna wa Manzon Allah (ﷺ) cewa al’ummarsa nan gaba za ta zama al’umma mai karatu da rubutu, watau mai alfahari da ilimi.
• Jan hankalinsa zuwa ga duba ga halittun Allah (Mai tsarki da daukaka), musamman halittar mutum mai cike da abin mamaki, wadda aka soma ta daga gudan jini.
• Kashedi ga wanda yake ta hanƙoron sai ya hana Manzon Allah (ﷺ) salla da kiran mutane zuwa ga gaskiya da shiriya.
• Nusantar da Manzon Allah (ﷺ) cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) yana sane da maƙiyansa, kuma lalle zai ba shi nasara a kansu, ya rusa duk wani shirinsu.
• Tabbatar da dugadugan Manzon Allah (ﷺ) a kan abin da ya zo masa na gaskiya da kusantar Allah (Mai tsarki da daukaka) da salla, kuma kada ƙarfin maƙiyansa ya dame, shi domin ƙarfin Allah ya zarce na kowa.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ ١ خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ ٢ ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ ٣ ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ ٤ عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ ٥
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta.
2. Ya halicci mutum daga gudan jini.
3. Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne mafi karamci.
4. Wanda Ya koyar ta (hanyar) alƙalami.
5. Ya koyar da mutum abin da bai sani ba.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzon Allah (ﷺ) ya yi karatu da sunan Ubangijinsa wanda ya halicci dukkan halittu. Ya halicci mutum daga gudan jini bayan a da yana ɗigon maniyyi.
Sannan ya sake umartar sa da ya karanta abin da aka yiwo masa wahayinsa na Alƙur’ani, ya kuma sani cewa, Ubangijinsa shi ne mafi karamci da babu wanda ya kai shi, saboda shi mai yawan kyauta ne da kyautatawa. Shi ne wanda ya koyar da ɗan'adam rubutu ta hanyar amfani da alƙalami, ya kuma sanar da shi abin da bai sani ba.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Waɗannan ayoyi biyar su ne farkon abin da aka yiwo wa Annabi (ﷺ) wahayinsa na Alƙur’ani, da su ne ya zama Annabin Allah.
2. Duk wani karatu ko ilimi wanda ba zai haɗa bawa da Ubangijinsa ba, ba kuma zai gadar masa da tsoron Allah ba, to wannan ilimi ne marar amfani ga ɗan’adam. Don haka kowane ilimi mutun zai koya, to ya sanya sunan Allah a ciki, kada kuma ya yarda ya raba shi da Ubangijinsa.
3. Wanda ya halicci mutum ya kula da shi da buƙatunsa, to dole ne a yi imani da kulawarsa gare shi, ta hanyar yi masa umarni da hani da aiko masa manzanni da saukar masa littattafai.
4. Babban karamcin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi wa ɗan’adam shi ne saukar masa da wahayi da sanar da shi ilimin abin da bai sani ba.
5. Falalar ilimi da muhimmancinsa, domin shi ne farkon abin da aka yi wa Manzon Allah (ﷺ) wahayi da shi, watau umartar sa da yin karatu.
6. Yawan karatu hanya ce ta samun ilimin abin da mutum bai sani ba.
7. Ishara ga al’ummar Larabawa waɗanda a lokacin ba sa rubutu ba sa karatu da cewa, ba da jimawa ba za su zama al’umma mai ilimi da za su cika duniya da rubuce-rubuce.
8. Ana samun ilimin komai ne ta hanyar koyon sa daga masanansa.
9. Muhimmancin rubuce-rubuce, domin ta haka ne ake tattara ilimi wuri guda kuma a kiyaye shi daga ɓacewa, sannan kuma ya shiga wurare da garuruwa masu nisa.
10. Tabbatar da cewa, Annabi (ﷺ) bai san Alƙur’ani ba kafin a yo masa wahayinsa, don haka aka kwantar masa da hankali da nuna masa cewa, kada ya fitar da tsammani, wanda ya koyar da mutane karatu da rubutu mai iko ne a kan ya koyar da shi Alƙur’ani, har ya zamanto makarancin sa ba tare da ya koyi rubutu ba.

***