87-Suratul A’ala
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura ta shahara da suna ‘Suratul A’ala’, saboda kalmar ‘Al-a’ala’ da ta zo a ayarta ta farko.
A lokacin Annabi (ﷺ) da sahabbai an fi sanin ta da ‘Sabbihisma Rabbikal A’ala’. An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Mu’azu ɗan Jabal ya yi wa mutanensa sallar isha’i ya tsawaita musu karatu sai wani ɗan saurayi ya kawo ƙarar sa wurin Manzon Allah (ﷺ), sai Manzon Allah (ﷺ) ya kira shi ya ce masa: “Shin kai fitinanne ne ya Mu’azu, me zai hana ka yi musu salla da ‘Sabbihisma Rabbika’ da ‘Was-Shamsi Wa Dhuhaha’ da ‘Wal-Laili Iza Yaghasha’ ?...” [Bukhari #705 da Muslim #465].
An karɓo daga Bara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Farkon wanda ya zo mana (watau mutanen Madina) shi ne Mus’ab ɗan Umairu da Ibn Ummi Maktum ((). Sun kasance suna karantar da mutane Alƙur’ani. Sai kuma Bilal da Sa’ad da Ammar ɗan Yasir (() suka iso. Sannan Umar ɗan Khaɗɗab (Allah ya kara masa yarda) ya zo tare da sahabban Manzon Allah (ﷺ) su ishirin. Sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya iso, ban taɓa ganin mutanen Madina sun yi farin ciki a kan wani abu ba kamar yadda suka yi farin ciki da zuwan Manzon Allah (ﷺ), har kuyangi ma sai da suka riƙa murna suna cewa: ‘Manzon Allah ya iso’. Annabi bai iso Madina ba har sai da na karanci ‘Sabbihisma Rabbikal A’ala’ da wasu surori na ‘Al-Mufassal’. [Bukhari #3925].
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya kasance yana yin wutiri da raka’a uku, yana karanta ‘Sabbihisma Rabbikal A’ala’ da ‘Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’ da ‘Ƙul Huwal-Lahu Ahad’.” [Ahmad #2725 da Tirmizi #462].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Sura ce Makkiyya a wurin malamai. Hadisin Bara’u da ya gabata yana tabbatar da haka.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta takwas (8) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratut Takwir’ kafin ‘Suratul Laili’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta goma sha tara (19) ne babu wani saɓani a kan haka.
5. Babban Jigonta:
Surar tana tunatar da mutane ne babbar baiwar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu da ƙarfafa alaƙarsu da ranar lahira da kuɓutar da su daga ƙyale-ƙyalen duniya.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tsarkake Allah (Mai tsarki da daukaka) da Kaɗaitakarsa da bauta saboda Kaɗaitakarsa wajen halittar ɗan’adam da halittar ɗaukacin abubuwan da suke bayan ƙasa na buƙatar ɗan’adam.
• Ƙarfafa gwiwar Manzon Allah (ﷺ) a kan karɓar wahayi daga Allah (Mai tsarki da daukaka).
• Tabbatar wa da Manzon Allah (ﷺ) cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba shi shari’a mai sauƙi, ya saukar masa da littafi wanda masu tsoron Allah suke wa’azantuwa da shi suke tsarkaka da karantarwarsa. Taɓaɓɓun mutane marasa rabo kuma suke bijire masa suna fifita rayuwar duniya ƙararriya a kan ta lahira mai ɗorewa.
• Lallashin Manzon Allah (ﷺ) game da muzgunawar da mushirikai suke yi masa da nuna masa cewa, littafin da Allah ya yi masa wahayinsa, dukkan littattafan da suka gabace shi suna gaskata shi.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
2. Wanda Ya yi halitta sai Ya daidaita (ta).
3. Wanda kuma Ya ƙaddara (abubuwa) sannan Ya shiryar (da halittarsa).
4. Wanda kuma Ya fitar da makiyaya.
5. Sai Ya mayar da ita duddugaggiya mai baƙi.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Annabi (ﷺ) da ya tsarkake Ubangijinsa mafi ɗaukaka, watau wanda yake sama da dukkan halittunsa, tare da furta sunansa lokacin ambaton sa da girmama shi.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya siffanta kansa da siffofi uku :
Na ɗaya, shi ne wanda ya yi halitta ya kuma daidaita halittar.
Na biyu, shi ne wanda ya ƙaddara wa kowace halitta jinsinta da nau’inta da siffofinta, ya kuma shiryar da kowane mahaluƙi zuwa ga abin da ya dace da shi.
Na uku, shi ne wanda ya fitar da abincin da dabbobi za su ci daga ƙasa, sannan ya mayar da shi duddugagge baƙi bayan da farko yana kore shar.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Umarni da yin tasbihi da tsarkake Allah (Mai tsarki da daukaka).
2. Tabbatar da ɗaukakar Allah (Mai tsarki da daukaka), ɗaukaka ta Zati da siffa da aiki.
3. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya halicci dukkan halittunsa masu rai ya kuma daidaita halittar kowannensu gwargwadon yadda ya dace da shi, sannan ya nuna masa abin da yake maslaharsa da amfaninsa, ya kuma sanar da shi yadda zai more shi.
4. Wanda ya yi halitta ya kuma hore mata rayuwarta shi ne wanda ya cancanta a bautawa shi kaɗai.
***
