77-Suratul Mursalat

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
An fi sanin wannan Sura da ‘Suratul Mursalati’, watau ana mata laƙabi da kalmar farko a cikinta.
A zamanin sahabbai ana kiran ta da sunan ‘Suratu Wal Mursalati Urfa’, kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari #3317 da Sahihu Muslim #2234.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Ummul Fadil (Allah ya kara mata yarda) ta ji shi yana karanta ‘Wal Mursalati Urfa’ sai ta ce: “Ya ɗana, wallahi karatun nan naka ya tuna min da karatun Manzon Allah (ﷺ) da na ji shi yana karanta wannan Surar, kuma ita ce ƙarshen abin da na ji Manzon Allah () yana karantawa a sallar magariba.” [Bukhari #765 da Muslim #462].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna ganin Sura ce Makkiyya, tana daga cikin surorin farko da aka saukar wa Manzon Allah () a Makka.
An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Yayin da muke tare da Manzon Allah () a wani kogo a Mina sai aka saukar masa ‘Wal Mursalati’, yana cikin karanta mini ita, bakinsa yana ɗanye da ita, sai kawai ga wata macijiya ta yiwo kanmu, sai Manzon Allah () ya ce: “Ku kashe ta.” Sai muka yi kanta, sai da sauri ta gudu, sai Manzon Allah () ya ce: “An tsare ta daga sharrinku, kamar yadda aka tsare ku daga sharrinta.” [Bukhari #1830 da Muslim #2234].
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta talatin da uku (33) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratul Humaza’ kafin ‘Suratu Ƙaf’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta hamsin ne (50) babu wani saɓani.
5. Babban Jigonta:
Tana tabbatar da aukuwar ranar alƙiyama da hujjoji masu ƙarfi, tare da tsoratarwa da gargaɗi ga masu ƙaryatawa.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Bayanin dalilin aukuwar tashi bayan mutuwa da wasu daga cikin alamomin alƙiyama.
• Kafa hujja da halittar ƙasa da ta mutum a kan yiwuwar tashi bayan mutuwa da alƙawarin narko ga masu ƙaryatawa.
• Yi wa masu ƙaryata tashin alƙiyama kashedi da aukuwar azaba a kansu tun a nan duniya kamar yadda aka hallakar da al’ummun da suka gabace su.
• Yi wa muminai alƙawarin kyakkyawan sakamako a lahira.
• Yin kira zuwa ga Musulunci da gaskata Alƙur’ani saboda dalilai bayyanannu a kan haka.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا ١ فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا ٢ وَٱلنَّـٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا ٣ فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا ٤ فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا ٥ عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا ٦ إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ ٧ فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ ٨ وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ ٩ وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ ١٠ وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ ١١ لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ ١٢ لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ ١٣ وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ١٤ وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ١٥
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Na rantse da iska mai bibiyar juna.
2. Da kuma iska mai tasowa da tsanani.
3. Da iska mai watso ruwa watsowa.
4. Da kuma (mala'iku) masu rarrabe ƙarya da gaskiya iya rarrabewa.
5. Sannan masu sauko da wahayi.
6. Don yanke hanzari ko don gargaɗi.
7. Lalle abin da ake yi muku alƙawari tabbas mai afkuwa ne.
8. To idan taurari aka shafe haskensu.
9. Idan kuma sama aka tsattsage ta.
10. Idan kuma duwatsu aka sheƙe su.
11. Idan kuma manzanni aka tattara su.
12. Ga wacce rana ce aka ƙayyaje musu.
13. Ga rana ta yin hukunci.
14. Me kuma ya sanar da kai ranar yin hukunci.
15. Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryatawa.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da rantsuwa da wasu muhimman halittunsa masu girma. Ya rantse da iska mai bibiyar juna, da iska mai tasowa da ƙarfi da iska mai watso da ruwa ƙasa.
Allah kuma ya yi rantsuwa da mala’iku masu saukowa da abin da yake rarrabe tsakanin gaskiya da ƙarya, watau masu saukowa da wahayi zuwa ga manzannin Allah domin yanke wa bayi hanzari a wurin Allah da wurin mutane ko gargaɗi ga mutane game da azabar Allah.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi waɗannan rantse-rantse ne don ya tabbatar da cewa, lalle alƙawarin tashi bayan mutuwa da hisabi da sakamako, tabbas mai aukuwa ne babu makawa.
Sai kuma Allah ya ambaci wasu alamomin wannan ranar da cewa, a lokacin da za a ga tsarin gudanar da duniya gaba ɗaya ya rikice, an tafiyar da hasken taurari, sama kuma ta tsattsage, mala’iku suna ta saukowa da umarnin Allah, an tumɓuke duwatsu daga wurarensu an dandaƙe su sun zama ƙura an sheƙe su; manzanni kuma an tattara su don wani ƙayyadajjen lokaci na wani yini mai girma, don su ba da shaida game da al’ummunsu cewa, sun isar musu da saƙon Allah, ranar da za a yi hukuncin tsakanin bayi a bayyana mai gaskiya da marar gaskiya da ɗan wuta da ɗan Aljanna.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa girman wannan rana har ya yi masa tambayar cewa, me ma ya sanar da shi ranar yin hukunci? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu ƙaryata manzannin Allah da gaskiyar da suka zo da ita.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana iya yin rantsuwa da duk abin da ya ga dama daga cikin halittunsa don ya nuna muhimmancinsa ya kuma janyo hankalin bayinsa don ɗaukar izina daga gare shi. Amma ba ya halatta ga wani mutum ya yi rantsuwa ba da Allah ba.
2. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi rantsuwa a nan da iska da kuma mala’iku saboda wata alaƙa da take tsakaninsu, watau iska takan taso ɗauke da rahamar Allah, watau ruwan sama. Su ma mala’iku sukan sauko da wahayi da ambaton Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda yake raya zukata da shi kamar yadda yake raya ƙasa da ruwan sama.
3. Hikimar saukar wa manzannin Allah wahayi ita ce yanke wa mutane duk wani hanzari a gaban Allah da gargaɗin su da azabarsa (Mai tsarki da daukaka).
4. Ambaton wasu alamomin tashin alƙiyama waɗanda suka haɗa da tafiyar da hasken taurari da tsattsagewar sama da niƙe duwatsu.
5. Tsoratar da masu ƙaryata ranar alƙiyama da azabar Allah mai tsanani.

***