72-Suratul Jinn

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura ta shahara da ‘Suratul Jinni’, saboda ta zo da labarin aljannu waɗanda suka saurari karatun Alƙur'ani daga Manzon Allah (ﷺ) suka ba da gaskiya. Imamul Bukhari a cikin ingantaccen littafinsa ya kira ta ‘Suratu Ƙul Uhiya Ilayya’, watau da kalmominta na farko.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Malamai sun haɗu a akan cewa Sura ce Makkiyya.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta arba’in (40) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratul A’arafi’, kafin ‘Suratu Yasin’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta ashirin da takwas ne (28) daidai.
5. Dalilin Saukarta :
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Annabi (ﷺ) ya fita tare da wasu sahabbansa suka nufi kasuwar Ukaz. A daidai wannan lokacin kuwa an hana shaiɗanu sato labari daga sama, an riƙa jifan su da harshen wuta na taurari. Sai shaiɗanun suka koma wajen jama’arsu, suka tambaye su: “Me ya faru gare ku?” Sai suka ce: “An hana mu sato labari daga sama ne, ana jifan mu da harshen wuta na taurari.” Sai ‘yan’uwansu suka ce: “Babu abin da ya hana ku samo labari daga sama sai wani babban al’amarin da ya faru, don haka ku bazama ku nufi gabashin duniya da yammacinta, ku duba ku ga mene ne ya hana ku samo labari daga sama?” Sai wasu daga cikinsu suka nufi nahiyar Tihama inda Annabi (ﷺ) ya iso wani wuri mai suna ‘Nakhla’ za su nufi kasuwar Ukazu, ya tsaya yana jan sahabbansa sallar Asuba. Yayin da aljannun nan suka ji ana karanta Alƙur’ani sai suka tsaya suka saurari karatunsa, sai kuwa suka faɗa wa junansu cewa: “Wallahi wannan ne ya hana mu samo labari daga sama.” To a nan ne suka juya suka koma zuwa ga jama’arsu suna cewa: “Ya ku jama’armu, lalle mun ji wani abin karatu mai ban mamaki.” Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa Annabinsa (ﷺ) faɗarsa: “Ka ce: An yiwo min wahayi cewa wata jama’a ta aljannu sun saurari (karatun Alƙur’ani).... an yi masa wahayin maganar aljannun ne kawai.” [Ahmad #2271 da Bukhari #773 da 4921 da Muslim #449].
6. Babban Jigonta:
Surar tana tabbatar da cewa, Alƙur’ani gaskiya ne, kuma wahayi ne daga Allah zuwa Manzonsa (ﷺ), aljannu kuma sun yi imani da shi.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da girman matsayin Annabi (ﷺ) da nuna cewa, da’awarsa ba ta tsaya iya mutane ba kaɗai, ta kai har ga aljannu waɗanda su ma sun saurari karatun Alƙur’ani kuma sun fahimce shi, sun kuma fahimci abin da yake koyarwa na Tauhidi da shiriya da sanin girman Allah da tsarkake shi daga a dangana masa mata ko ɗa ko wani abokin tarayya.
• Rushe bautar aljannu da wasu suke yi.
• Rushe bokanci da da’awar sanin gaibi, sai manzannin da Allah ya zaɓa ya sanar da su abin da ya ga dama daga ɓoyayyen iliminsa.
• Tabbatar da samuwar wasu halittun Allah da ake kiran su ‘aljannu’ waɗanda a cikinsu akwai nagari akwai na banza kashi-kashi.
• Bayanin ɓatar duk masu yi wa Allah ƙarya suna jingina masa abin da bai faɗa ba, da masu bautar aljannu da masu ƙaryata tashi bayan mutuwa da nuna musu cewa, aljannu ba za su iya kuɓuce wa ikon Allah ba.
• Mamakin aljannu na ganin ana jifan su da harshen wuta idan sun nufi sararin sama don su sato labari.
• Sukan mushirikai masu hana a tsarkake Allah da bauta a cikin masallatan Allah da gargaɗin su da cewa, za su yi nadama a kan yunƙurinsu na cutar da Manzon Allah (ﷺ) da sukan addininsa.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
قُلۡ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ ٱسۡتَمَعَ نَفَرٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَقَالُوٓاْ إِنَّا سَمِعۡنَا قُرۡءَانًا عَجَبٗا ١ يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلرُّشۡدِ فَـَٔامَنَّا بِهِۦۖ وَلَن نُّشۡرِكَ بِرَبِّنَآ أَحَدٗا ٢ وَأَنَّهُۥ تَعَٰلَىٰ جَدُّ رَبِّنَا مَا ٱتَّخَذَ صَٰحِبَةٗ وَلَا وَلَدٗا ٣ وَأَنَّهُۥ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى ٱللَّهِ شَطَطٗا ٤ وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن تَقُولَ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا ٥ وَأَنَّهُۥ كَانَ رِجَالٞ مِّنَ ٱلۡإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٖ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَزَادُوهُمۡ رَهَقٗا ٦ وَأَنَّهُمۡ ظَنُّواْ كَمَا ظَنَنتُمۡ أَن لَّن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ أَحَدٗا ٧
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka ce: “An yiwo min wahayi na cewa, wata jama’a ta aljannu sun saurari (karatun Alƙur’ani), sai suka ce: “Lalle mu mun ji Alƙur’ani mai ban mamaki.
2. “Yana shiryarwa zuwa ga daidai, saboda haka muka yi imani da shi; ba kuwa za mu haɗa wani da Ubangijinmu ba har abada.
3. “Kuma lalle yadda lamarin yake, girman Ubangijinmu ya ɗaukaka, bai riƙi wata mata ko wani ɗa ba.
4. “Kuma lalle yadda lamarin yake, wani wawa daga cikinmu ya kasance yana faɗar mummunar ƙarya game da Allah.
5. “Lalle kuma mun yi tsammanin mutum da aljan ba za su taɓa faɗar ƙarya game da Allah ba.
6. “Kuma lalle yadda lamarin yake, wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari daga wasu mazaje na aljannu, saboda haka suka ƙara musu girman kai.
7. “Kuma lalle su sun yi tsammanin-kamar yadda kuka yi tsammani-cewar Allah ba zai tashi kowa ba har abada.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) ya faɗa wa al’ummarsa cewa, an yiwo masa wahayi game da wasu jama’a na aljannu waɗanda suka saurari karatunsa na Alƙur’ani mai girma a wani wuri da ake kira Baɗnu Nakhla, lokacin da yake yi wa sahabbansa sallar Asuba. Bayan sun gama sauraro sai suka koma wajen jama’arsu ta aljannu suna gaya musu cewa, lalle sun saurari wani abin karatu mai ban al’ajabi, yadda yake cike da fasaha da hikima. Yana kuma shiryarwa zuwa ga ingantacciyar aƙida da kyakkyawan aiki da kyawawan maganganu, don haka su sun yi imani da shi, kuma daga lokacin ba za su ƙara haɗa Allah da wani ba wajen bautarsu.
Sun kuma yi imani da cewa, girman Ubangijinsu ya ɗaukaka, bai kuma riƙi wata mata ko ɗa ba, kamar yadda mushirikansu na aljannu da na mutane suke riyawa. Suka kuma tabbatar wa da jama'arsu cewa, maganar da wawan cikinsu yake yi, watau Iblisu da ire-irensa na yi wa Allah ƙarya da jingina masa mata da ɗa mummunar ƙarya ce suke ƙirƙira masa. Suka kuma bayyana cewa, da farko sun zaci mushirikan mutane da na aljannu ba za su taɓa yi wa Allah ƙarya ba ballantana har su riƙa cewa yana da mata da ɗa, wannan ne ya sa har suka ɗauki maganarsu a matsayin gaskiya, sai suka bi su ido-rufe.
Sannan suka bayyana wata mummunar aƙida ta wasu mutane waɗanda, a lokacin jahiliyya idan sun yi tafiya sun sauka a wani wuri mai ban tsoro, kamar wani kwari, sukan nemi tsarin wasu mazajen aljannu, watau ɗayansu yakan ce, yana neman shugaban wannan kwarin ya kare shi daga sharrin wawayen jama’arsa. Wannan lamari ya janyo mazajen mutane suka ƙara firgita da tsorata daga mazajen aljannu.
Suka kuma tabbatar wa da jama'arsu cewa, sun gano cewa, kamar yadda su aljannu suka yi zaton babu wanda Allah zai tashe shi domin yi masa hisabi, hakanan su ma mutane suka yi wannan zaton. Watau wannan mummunan zato nasu ne ya sanya su yin shirka da Allah da ɗagawa a bayan ƙasa.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Alƙur’ani littafi ne mai saurin ratsa zuciya ga duk wanda ya tsaya da zuciya ɗaya ya saurare shi, mutum ne shi ko aljani.
2. Aljannu halitta ce da suke a ɓoye, mutum ba ya iya ganin su a siffarsu ta aljannu sai dai su suna ganin kowa, don haka shi kansa Manzon Allah (ﷺ) bai gan su ba lokacin da suke kusa da shi suna sauraron karatunsa na Alƙur’ani har sai da Allah ya yiwo masa wahayi ya sanar da shi.
3. Annabi Muhammad (ﷺ) bawan Allah ne kuma Manzonsa, yana karɓar umarni ne daga Allah mahaliccinsa, yana bin dokarsa.
4. Annabi Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne zuwa ga mutane da aljannu baki ɗaya.
5. Daga cikin aljannu akwai waɗanda suka yi imani da Allah, akwai kuma mushirikai.
6. Waɗannan aljannun da suka saurari karatun Alƙur’ani daga Manzon Allah (ﷺ), wasu aljannu ne da suka fito daga garin Nasibin na ƙasar Sham, watau Siriya a yau, kuma suna magana da harshen Larabci ne wanda hakan ya ba su damar fahimtar Alƙur’ani yayin da suka saurari karatunsa.
7. Alƙur’ani littafi ne da yake cike da hikima da fasaha mai ban al’ajabi matuƙa.
8. Alƙur’ani littafin shiriya ne, yana nuna wa mutane da aljannu aƙidu na gaskiya da kyawawan ayyuka da maganganu da halaye.
9. Waɗannan aljannun sun kasance a da mushirikai ne sai bayan sun ji karatun Alƙur’ani ne suka yi imani.
10. Waɗannan aljannun sun nuna kyakkyawar aniyarsu, don haka suka gaskata faɗarsu da aiki, yayin da suka yi alƙawarin cewa ba za su ƙara haɗa wani da Allah ba, bayan da farko sun ce sun yi imani.
11. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsarkaka daga duk wani aibi ko naƙasa, kamar buƙatar mata ko ɗa.
12. Daga cikin aljannu akwai masu cewa Allah yana da mata da ɗa.
13. Daga cikin aljannu akwai maƙaryata, kamar yadda ake da su a cikin mutane.
14. Daga cikin aljannu akwai maza akwai mata.
15. Danganta kowace matsala da aljannu da neman taimako a wurinsu abu ne da yake ƙara sanya su ɗagawa, sai suka sanya rayuwar mutane cikin tsoro da firgici.
16. Neman tsari da aljannu shirka ce kuma haramun ne.
17. Duk wata mummunar aƙida da take cikin mutane akwai irinta a cikin aljannu, hakanan duk wani alheri da ke cikin mutane akwai shi a cikin aljannu.

***