7-Suratul A’araf
Mabuɗin Surar:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da suna ‘Suratul A’araf’. An ba ta wannan suna ne kuwa saboda an ambaci wannan lafazin a cikinta. Watau an yi bayanin mutanen tozon La’arfi a lahira, babu kuma inda aka yi bayaninsu sai a wannan Surar.
An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya karanta Suratul A’raf a sallar Magriba, ya kuma raba ta biyu a cikin raka’o’insa biyu.
An karɓo daga Zaidu ɗan Sabitu (Allah ya kara masa yarda) ya ce wa Marwan ɗan Hakam: “Mene ne ya sa nake ganin ka a sallar Magriba kana karanta gajejjerun surori, alhalin haƙiƙa ni na ga Manzon Allah a sallar Magriba yana karanta ɗaya daga cikin dogayen surorin nan biyu?” Sai Marwan ya tambaye shi: “Wacce Sura ce wannan mai tsawo?” Sai ya ce masa: “Al-a’raf”.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Wannan Sura Makiyya ce, kamar yadda wasu malamai suka ambato ijma’i a kan hakan.
3. Jerin Saukarta:
Ana lissafa ta a Sura ta talatin da tara (39) a jerin saukar surori. Ta sauka bayan ‘Suratu Sad’, gabanin ‘Suratul Jinn’.
4. Adadin Ayoyinta:
A lissafin mutanen Madina da Kufa adadin ayoyinta ɗari biyu ne da shida (206). Amma a lissafin mutanen Sham da Basra, ayoyinta ɗari biyu da biyar ne (205).
5. Babban Jigonta:
• Lallashin Annabi (ﷺ) game da ƙaryata shi da kafirai suke yi.
• Bayanin jigogin aƙida da manya-manyan ƙa’idoji na addini.
• Bayanin dogon zangon da ‘yan’adam suka keto tun farkon halittar Annabi Adamu har zuwa tashin alƙiyama.
6. Daga Cikin Abubuwa Da Ta ƙunsa Akwai:
• Ishara zuwa ga girman darajar Alƙur’ani mai girma.
• Hana bautar wasu tare da Allah da gargaɗin mushirikai a kan mummunar makomar shirka a duniya da lahira da bayanin azabar da ta auka wa mushiriai da masu ƙaryata manzanni a nan duniya da abin da zai same su a lahira da kafa dalilai masu nuna Ɗayantakar Allah.
• Magana a kan auna ayyukan mutane a lahira da tuna musu ni’imomin da Allah ya yi musu a bayan ƙasa ya hore wa ɗan’adam amfani da su.
• Bayanin halittar Annabi Adamu da abin da ya biyo bayanta na sujjadar mala’iku a gare shi domin biyayya ga Allah da bijirewar Shaiɗan da yadda ya bayyana tsananin hassadarsa da gabarsa ga Annabi Adamu da zurriyarsa da alwashin da ya ɗauka a gaban Allah na cewa sai ya hallaka su in ban da zaɓaɓɓun bayinsa. Da bayanin yadda ya fara da saka waswasi ga Adamu da matarsa Hauwa’u (() har suka ci itaciyar da Allah ya hana su ci, aka saukar da su a doron ƙasa baki ɗaya.
• Magana a kan ƙissar mutanen tozon La’arafi da tunatarwa a game da tashin alƙiyama.
• Hani a kan yaɗa ɓarna a bayan ƙasa bayan Allah ya gyara ta don amfanin ɗan’adam.
• Ambaton labaran manzannin Allah tare da mutanensu tun daga Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) har zuwa Musa da Fir’auna da mutanensa.
• Tsoratarwa game da amincewa da makircin Allah, yayin da jinkirta wa masu laifi zai sa su su ruɗu su zarme cikin saɓon Allah.
• Bushara da aiko Annabi (ﷺ) da ambaton wasu daga cikin siffofinsa a littattafan Attaura da Linjila.
• Umartar Musulmi da ɗabi’antuwa da wasu halaye masu kyau, kamar yin afuwa da yafiya da kuma ci gaba da ƙoƙari wajen kira zuwa ga Allah da haƙuri a kan haka.
• Da sauran mahimman batutuwa da Surar ta ƙunsa.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Alif Laam Miim Saad.
2. (Wannan) Littafi ne da aka saukar maka, don haka kada wani ƙunci ya kasance a ƙirjinka a sanadiyyarsa, don ka yi gargaɗi da shi, kuma da tunatarwa ga muminai.
3. Ku bi abin da aka saukar muku daga Ubangijinku, kada kuma ku bi wasu masoya ba shi ba. Kaɗan ne ƙwarai kuke wa’azantuwa.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar mai girma da haruffa irin waɗanda ya buɗe surorin Al-Baƙara da Ali Imrana da su. Malaman tafsiri sun yi batutuwa masu yawa a kan bayanin manufofin waɗannan haruffa. Magana mafi rinjaye ita ce mai cewa, waɗannan harrufa an kawo su ne don bayyana mu’ujizar Alƙur’ani, wato shi littafi ne da ya ƙunshi haruffan da Larabawa suke magana da rubutu da su. To idan suna ganin Alƙur’ani ba daga Allah yake ba, to su kawo wata magana kwatankwacinsa idan za su iya. Shi ya sa a duk inda aka buɗe wata Sura da waɗannan haruffa, to magana a kan Alƙur’ani ne takan biyo bayansu, domin alaƙar da ke tsakaninsu.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗa wa Annabi (ﷺ) cewa, Alƙur’ani littafi ne da ya saukar masa, don haka kada ya samu wani ƙunci a ƙirjinsa game da isar da saƙon da yake cikinsa, kuma ya yi gargaɗi da wa’azi da shi, kada ya yi shakkar kasancewarsa saukakke ne daga Allah (Mai tsarki da daukaka). Allah ya saukar da shi ne domin ya tsoratar da kafirai da shi, ya kuma zama wa’azi ga muminai.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci mutane da su bi abin da ya zo a wannan Alƙur’ani, kuma su yi aiki da shi, kada su bi wasu majiɓinta ba shi ba, sai su raba su da koyarwar Alƙur’ani da sunnar Manzo (ﷺ). Allah ya ba da labarin cewa, kaɗan ne masu wa’azantuwa su ɗauki darasi su koma ga gaskiya.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Wajibi ne ga Musulmi ya riƙa tuntuntuni game da Alƙur’ani, yana fahimtar umarninsa da haninsa da abin da ya halatta da abin da ya haramta ya yi aiki da su, ya tabbatar da abin da yake cikinsa na ingantacciyar aƙida.
2. Kada wani Musulmi ya riƙe wasu ba Allah ba yana bin su sau-da-ƙafa kamar yadda ake bin Allah da Manzonsa (ﷺ). Wanda duk ya yi haka, to ya nesanta kansa daga Allah da Manzonsa (ﷺ).
3. Alƙur’ani ya zo ne don ya kawar da duk wani ƙunci ko damuwa ta zukata, don haka duk wanda ya riƙe shi, to zai samu cikakkiyar waraka daga duk wani ƙuncin zuciya da damuwa.
***
