5-Suratul Ma’ida

Mabuɗin Surar:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da suna ‘Suratul Ma’ida’, saboda a cikin ta an kawo bayanin ‘Ma’ida’, wato kaɓaki na abinci wanda Hawariyyuna almajiran Annabi Isa suka nemi ya roƙi Allah a saukar musu da shi don su ci daga gare shi kuma su ƙara yarda da ingancin annabcinsa.
An karɓo daga Jubairu ɗan Nufairu (Allah ya kara masa yarda.) ya ce: “Na je hajji sai na shiga wajen A’isha (Allah ya kara mata yarda) sai ta ce mini: “Ya Jubairu, kana karanta Al-Ma’ida?” Sai na ce: “E.” Sai ta ce: ‘Lalle ita ce ƙarshen Surar da ta sauka.’….” [Ahmad #25547, da Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #1073].
Ana kiran ta da ‘Suratul Uƙūd’, domin zuwan wannan lafazin a farkon Surar.
2. Sanda Ta Sauka:
Malamai sun haɗu a kan cewa a Madina aka saukar da ita.
Hadisin Jubairu ɗan Nufairu daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ya gabata.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta tis’in da ɗaya (91) a jerin saukar surori. Ta sauka bayan ‘Suratul Ahzab’, gabanin ‘Suratul Mumtahana’.
4. Adadin Ayoyinta:
A lissafin yawancin malamai ayoyinta ɗari ne da ashirin da biyu (122), amma a lissafin mutanen Basra adadinsu ɗari ɗaya ne da ashirin da uku (123), a wurin mutanen Kufa kuwa ayoyinta ɗari ne da ashirin (120) daidai.
5. Falalarta:
Tana daga cikin dogwayen Surori da aka ba wa Annabi (ﷺ) maimakon At-Taura:
An karɓo daga Wasila ɗan Al-Asƙa’ (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “A madadin Attaura an ba ni dogwayen surori bakwai. A madadin Zabura kuwa an ba ni surori masu ayoyi ɗari (ko ɗoriya). A madadin Linjila kuwa an ba ni Al-Masani. Sannan an fifita ni da (surorin) Mufassal.”
Tana daga cikin abin da ya sauka na ƙarshe a Alƙur’ani:
An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Surar ƙarshe da ta sauka ita ce ‘Suratul Ma’ida’.” [Tirmizi #3063].
6. Babban Jigonta:
• Ƙarfafa batun cika alƙawari da yarjejeniya.
• Bayanin wasu al’amuran aƙida masu yawa.
• Bayanin wasu da dama daga cikin hakunce-hukuncen shari’a.
• Tsara alaƙa tsakanin Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da ingantacciyar aƙida da ba wa mas’alolin Tauhidi muhimmanci da tunatarwa game da ranar alƙiyama.
• Gargaɗi a kan jiɓintar waɗanda ba Musulmi ba da bayanin cewa munafukai su ne suka fi saurin rungumar kafirai.
• Tsara alaƙa tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, musamman ma Yahudu da Nasara.
• Bayanin wasu daga cikin hukunce-hukuncen shari’a masu alaƙa da ibada ko mu’amala, kamar hukunce-hukuncen yarjejeniya da yanka da farauta da ihrami da auren mace Bakitabiya da hukuncin ridda da na tsarki da haddin sata da ta’addanci da yaɗa ɓarna a bayan ƙasa da haramcin giya da caca da kaffarar rantsuwa da wasiyya lokacin mutuwa da sauransu.
• Surar ta ƙunshi wasu labarai na Banu Isra’ila tare da Annabi Musa, da ƙissar ‘ya’yan Annabi Adamu da ƙissar saukar da kaɓaki ga Banu Isra’ila.
• Bayanin wasu daga cikin miyagun halayen Yahudawa da Nasara kamar karya alƙawari da canja Littattafan Allah da jingina wa Allah ɗa da ƙaryata manzancin Annabi Muhammadu (ﷺ).

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَوۡفُواْ بِٱلۡعُقُودِۚ أُحِلَّتۡ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلۡأَنۡعَٰمِ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ غَيۡرَ مُحِلِّي ٱلصَّيۡدِ وَأَنتُمۡ حُرُمٌۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ مَا يُرِيدُ ١ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحِلُّواْ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَلَا ٱلۡهَدۡيَ وَلَا ٱلۡقَلَـٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّهِمۡ وَرِضۡوَٰنٗاۚ وَإِذَا حَلَلۡتُمۡ فَٱصۡطَادُواْۚ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ ٢
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ya ku waɗanda suka yi imani, ku cika alƙawura. An halatta muku dabbobin ni’ima, sai dai abin da ake karanta muku (haramcinsa), ba kuna masu halatta farauta ba alhalin kuna cikin Harami, lalle Allah Yana hukunta abin da Yake nufi.
2. Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku halatta keta alfarmar alamomin addinin Allah, ko (ku wulaƙanta) Wata mai alfarma ko dabbobin hadaya ko dabbobin hadaya masu alama da (tare) masu nufin ziyarar Ɗaki mai alfarma, suna neman falala daga wurin Ubangijinsu da yardarsa. Idan kuwa kuka kwance Harami, to ku yi farauta (idan kuna so). Kuma kada ƙiyayyar wasu mutane da suka hana ku isa masallaci mai alfarma, ta sa ku yi ta’addanci. Kuma ku taimaki juna a kan aikin alheri da taƙawa; kada kuma ku taimaka wa juna a kan ayyukan saɓo da ta’addanci. Kuma ku kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar ne da umartar muminai kansu riƙa cika alƙawurran da suka ɗauka tsakaninsu da Allah da waɗanda suke tsakaninsu da ‘yan’uwansu mutane, amma alƙawuran da ba su saɓa wa shari’a ba. Sannan kuma ya bayyana musu cewa, ya halatta musu dabbobin ni’ima, irin su raƙuma da shanu da ƙananan dabbobi, sai dai waɗanda za a yi musu bayanin su nan gaba a aya ta 3. Kuma ba a halatta musu yin farauta ba lokacin da suke sanye haramin hajji ko umara, ko kuma sanda suke cikin Haramin Makka da Madina. Allah kuma yana hukunta abin da ya yi nufi ne, ya kuma zartar da hukuncin da ya ga dama.
Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya haramta wa muminai ƙetare iyakokinsa ta hanyar wulaƙanta abubuwa masu alfarma waɗanda ya yi umarnin a girmama su na addini, kamar ayyukan hajji da umra da kuma watannin nan masu alfarma, watau Shawwal da Zulƙi’ida da Zulhijja da Rajab, ta hanyar yin yaƙi a cikinsu ko aikata zalunci ko wasu laifuffuka. Hakanan ya haramta musu keta alfarmar dabbobin da aka ware don hadaya ta hanyar su yanka su kafin su ƙarasa mayankansu, ko kuma su hana dabbobin ƙarasawa can; haka kuma dabbobin da aka yi musu alamomi da rataye a wuyansu domin nuna cewa an keɓance su don yankan hadaya. Hakanan Allah ya hana muminai yaƙar waɗanda suka taho domin ziyarar Ɗakin Ka’aba don neman falarar Allah da yardarsa, wato masu niyyar hajji da umara ko niyyar kasuwanci, saboda duk wanda ya shiga garin Makka, to ya zama amintacce. Amma kuma Allah ya halatta musu su yin farauta yayin da suka sauke hiraminsu na hajji ko na umara da kuma lokacin da suka fita daga Haramin Makka ko Madina.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kada ƙiyayyar mutanen da suka cuce su suka hana su shiga garin Makka ta sa su su zalunce su ko su yi musu ta’addanci, domin shi mumini dole ne a komai ya ji tsoron Allah, kuma ya zama mai gaskiya.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce su da su taimaki junansu a kan aikin alheri da taƙawa, kada su taimaki juna a kan aikata zunubi da zalunci, ya umarce su da su ji tsoron Allah ta hanyar aikata abin da ya yi umarni da shi da barin abin da ya hana. Lalle Allah mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya saɓa masa.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Duk wata yarjejeniya wadda ba ta saɓa wa shari’a ba, wadda mutum biyu ko fiye ko ɓangarori biyu za su ƙulla, to wajibi ne kowa ya riƙe ta kada ya karya ta da gangan.
2. Wajibi ne ga mumini ya miƙa wuya ga hukuncin Allah, ba tare da jayayya ko ɓata rai ba.
3. Faɗakarwa a kan girmama wuraren ibada masu alfarma da watanni masu alfarma, domin girmama su girmama Allah (Mai tsarki da daukaka) ne.
4. Musulunci yana umartar ‘ya’yansa da su zama masu adalci hatta ga maƙiyansu waɗanda suka cuce su. Kada ƙiyayyar macuci ta kai su ga hana masa haƙƙinsa ko ƙetare iyaka wajen karɓo haƙƙinsu da yake hannunsa, ta hanyar ƙwatar fiye da abin da ya halatta a karɓa daga wajensa. Domin Musulunci yana so ‘ya’yansa su zama daban wajen kyawawan halaye da ɗabi’u, ta yadda maƙiyi zai fahimci haƙiƙanin koyarwar addinin Musulunci daga halayyar Musulmi su kansu.
5. Musulunci yana kira zuwa ga samun taimakon juna cikin al’umma a kan ayyukan alheri domin gina nagartacciyar al’umma a bayan ƙasa, kamar yadda ya haramta duk wani aikin haɗin kai wajen saɓa wa Allah da Manzonsa (ﷺ) ko cutar da wasu.