33-Suratul Ahzab
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da suna ‘Suratul Ahzab’. Ba ta da wani suna sai wannan. Al-Ahzab yana nufin gangamin rundunoni. An sa mata wannan suna ne saboda a cikinta ne Allah ya yi bayanin gangamin rundunonin kafiran Ƙuraishawa da ƙawayensu waɗanda suka nufi yaƙar Musulmi a Madina, amma Allah ya rusa makircinsu, ya tarwatsa su.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Malamai sun yi ittifaƙi a kan cewa Sura ce Madaniyya.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta tis’in (90) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta kuma sauka bayan ‘Suratul Anfal’ kafin ‘Suratul Ma’ida’.
4. Adadin ayoyinta:
Ayoyinta saba’in da uku ne (73) babu wani saɓani.
5. Babban Jigonta:
Wajbacin yi wa Allah (Mai tsarki da daukaka) da Manzonsa (ﷺ) ɗa'a a kowane hali da guje wa saɓa wa umarninsu.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Yawancin ayoyinta suna mayar da martani ne ga munafukai masu faɗar miyagun maganganu game da Manzon Allah da nufin su cutar da shi, kamar maganganunsu a kan aurensa da Zainab ‘yar Jahshi.
• Allah ya yi bayanin hukuncin ɗan riƙo da rushe al’adar jahiliyya a kan haka.
• Surar yi magana a kan al’adar Larabawa ta cin gadon juna ta hanyar ƙawance ko hijira, inda aka rushe wannan al’ada.
• Ta yi nuni zuwa ga girman matsayin Annabi (ﷺ) a wurin muminai da cancantarsa gare su fiye da kawunansu.
• Ta kwaɗaitar da muminai a kan su rungumi shari’ar Allah su yi aiki da ita, domin haka shi ne alƙawarin da Allah ya yi da ilahirin annabawansa.
• Bayyana kariyar Allah ga muminai da ba su nasara a kan maƙiyansu waɗanda suka yi gangami domin su ga bayansu.
• Yabo ga muminai a kan gaskiyarsu da jajircewarsu don ba wa addinin Allah kariya.
• Bayanin ni’imar da Allah ya yi wa muminai yayin da ya mallaka musu garuruwan Ahlulkitabi waɗanda suka taimaka wa rundunonin kafirci.
• Bayani a kan hukunce-hukuncen da suka shafi zamantakewar aure na matan Manzon Allah (ﷺ), da bayanin falalarsu da falalar sauran iyalan gidan Manzon Allah (ﷺ) da sauran Musulmi mutanen kirki maza da mata.
• Hukuncin iddar matar da aka saki kafin tarewarta.
• Batu game da matan da suka halatta Annabi (ﷺ) ya aura da kuma hukuncin hijabi ga matansa Ummahatul Mu’uminina da suturar ‘ya mace Musulma.
• Razanarwa ga munafukai masu yayata ji ta-ji ta a Madina da niyyar tayar wa da Musulmi hankali.
• Kwaɗaitar da Musulmi a kan yawan ambaton Allah da kuma girmama Manzonsa (ﷺ) da yi masa salati.
• Alƙawarin narkon azaba ga munafukai masu cutar da Allah da Manzonsa da muminai.
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ya kai wannan Annabi, ka kiyaye dokokin Allah, kada ka yi wa kafirai da munafukai ɗa'a. Lalle Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima.
2. Kuma ka bi abin da ake yi maka wahayinsa daga Ubangijinka. Lalle Allah Ya kasance Masanin abin da kuke aikatawa ne.
3. Ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa wakili.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da kira ga Annabi (ﷺ) da umartar sa a kan ya dawwama a kan aiki da umarninsa da guje wa haninsa. Ya kuma hana shi yin biyayya ga kafirai da munafukai a kan abin da zukatansu suke so wanda ya saɓa wa shari’ar Allah. Allah ya tabbatar da cewa shi masanin duk abin da kafirai da munafukai suke ƙullawa ne, mai hikima ne a halittarsa da tsare-tsarensa da shari’arsa.
Sannan Allah ya umarce shi da bin abin da ya saukar masa na wahayi shi da al’ummarsa, ya tabbatar musu cewa shi masanin duk abin da suke aikatawa ne kuma zai yi musu sakayya a kan ayyukansu baki ɗaya.
Sai kuma ya umarce shi da ya dogara ga Allah shi kaɗai cikin dukkan al’amuransa, domin kuwa shi Allah ya isa ya zamanto wakili mai tsare bayinsa waɗanda suka dogara da shi.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kirawo Annabinsa (ﷺ) da siffar annabta ba kamar yadda yake kiran sauran annabawa da sunayensu ba. Wannan yana nuna girman martabar Manzon Allah (ﷺ) da fifikonsa a kan sauran annabawa, da kuma koyar da al’ummarsa yin ladabi a gare shi yayin ambatonsa, watau kada su kirawo shi da tsurar sunansa babu lafazin girmamawa a ciki, yin haka ba ladabi ne ba.
2. Wajabcin taƙawa, watau aiki da umarnin Allah da guje wa haninsa, domin kare kai daga azabarsa.
3. Nuni a kan cewa babu wani wanda ya fi ƙarfin a yi masa nasiha ko wa’azi, domin ga shi an yi wa Manzon Allah (ﷺ) duk da yawan tsoron Allah da yake da shi.
4. Annabi (ﷺ) bawan Allah ne da aka umarce shi da bin shari’a da riƙo da ita. Don haka babu wani matsayi da bawa zai taka na tsoron Allah har da hukunce-hukuncen shari’a za su sauka daga kansa. Duk wanda yake ganin akwai wani mutum da zai kai matsayin da shari’a za ta sauka daga kansa, to wannan ya ɓata ɓata mabayyani.
5. Haramcin yin biyayya ga kafirai da munafukai da miƙa wuya ga duk wasu buƙatunsu.
6. Wajabcin bin abin da Allah ya saukar na Alƙur’ani da gabatar da shi a kan duk wata fahimta.
7. Gargaɗi da tsoratarwa game da saɓa wa Allah domin Allah masanin duk abin da mutane suke aikatawa ne.
8. Wajabcin dogaro ga Allah shi kaɗai, domin shi ne fiyayyen mai ba da kariya ga bayinsa.
***
