29-Suratul Ankabut

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da ‘Suratul Ankabut ’. Al-Ankabut yana nufin gizogizo, wanda aka ambace shi a cikinta a aya ta 41.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna ganin Sura ce Makkiyya. An sami saɓani a kan ayoyinta goma sha ɗaya na farko, wasu malamai suna ganin sun sauka ne a Madina, domin an buɗe Surar da magana da muminai da yin gargaɗi a kan munafunci a aya ta 11; munafunci kuwa ya ɓullo ne a Madina ba a Makka ba.
Daga ayoyinta kuma za a iya fahimtar kasancewarta Makkiyya, domin a ciki Allah ya yi magana a kan kafirai da batun mu’ujizar Alƙur’ani da bayyana ƙissoshin wasu annabawa domin ɗaukar izina da darasi da batun azabar lahira ga masu girman kai masu bijire wa gaskiya.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta tamanin da biyar (85) a jerin saukar surori, ta sauka bayan Suratur Rum gabanin Suratul Muɗaffifin. Tana cikin surorin ƙarshe da suka sauka a Makka kafin hijira.
4. Adadin ayoyinta:
Duk malamai sun haɗu a kan cewa adadin ayoyinta sittin da tara (69) ne.
5. Babban Jigonta:
Surar tana nuna cewa imani ba kalma ce da ake faɗar ta da fatar baki kawai ba. Imani yana buƙatar haƙuri da juriya a kan abin da mumini zai fuskanta na fitintinu da tsangwama saboda imaninsa, don haka yana buƙatar jajircewa har ya kai ga cin nasara.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da muminai waɗanda mushirikai suke ta fitinar su don ƙoƙarin hana su addinin Musulunci.
• Alƙawarin Allah na taimakon muminai da wulaƙanta mushirikai da mataimakansu daga cikin ma’abota littafi.
• Umarni a kan nisantar mushirikai ko da kuwa makusanta ne.
• Wajabcin yin haƙuri a kan cutarwar mushirikai da nuna wa muminai cewa ƙasar Allah tana da yalwa, suna iya yin hijira domin tsira da addininsu.
• Jayayya da ma’abota littafi ta hanyar da ta dace in ban da waɗanda suke zaluntar muminai daga cikinsu.
• Umarni ga Annabi (ﷺ) a kan ya dage wajen isar da saƙon Alƙur’ani da shari’un Musulunci.
• Ɗaukan darasi daga al’ummu da manzanninsu da suka gabata da bayanin cewa shi ma Manzon Allah (ﷺ) ya zo ne da irin abin da sauran manzanni suka zo da shi.
• Kafa dalili mai ƙarfi a kan cewa Alƙur’ani saukakke ne daga Allah, idan aka lura da cewa Annabi mutum ne ummiyyi ba ya rubutu ba ya karatu.
• Tunatar da mushirikai irin ni’imomin da Allah ya yi musu domin su watsar da bautar wasu gumaka ba Allah ba, su bauta wa Allah shi kaɗai wanda suka yarda da cewa shi ne mahaliccin kowa da komai a sammai da ƙasa.
• Kafa hujja a kan yiwuwar tashi bayan mutuwa, domin ƙirƙirar halitta daga babu ya fi zama abin mamaki a kan sake dawo da ita bayan mutuwa.
• Tabbatar da sakamakon ayyuka a ranar alƙiyama.
• Bayar da misali na kafiran da suka riƙi wasu abubuwan bauta ba Allah ba da misalin gidan gizo-gizo mai matuƙar rauni.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
الٓمٓ ١ أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ ٢ وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ ٣ أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَسۡبِقُونَاۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ ٤
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. ALIF LAM MIM.
2. Yanzu mutane suna tsammanin za a ƙyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?
3. Haƙiƙa kuwa Mun fitini waɗanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waɗanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maƙaryata.
4. Ko kuma waɗanda suke aikata munanan ayyuka suna tsammanin za su gagare Mu ne? Abin da suke hukuntawa ya munana.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da haruffa kamar yadda ya yi a wasu surori da suka gabace ta [Dubi farkon Suratul Baƙara a wannan tafsirin domin ƙarin bayani].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa yanzu mutane za su yi tsammani a bar su hakanan ba a jarrabi gaskiyar imaninsu ba don kawai sun furta da baki cewa sun yi imani? Watau abin ba haka yake ba, lalle sai an jarraba su.
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa ya jarrabi al'ummun da suka gabaci wannan al’umma, kuma yana yin haka ne domin ya rarrabe tsakanin masu gaskiya cikin da’awar imaninsu a fili a san su, da kuma maƙaryata.
An karɓo daga Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi Manzon Allahا (ﷺ) cewa: Waɗanne mutane ne jarrabawarsu ta fi tsanani?” Sai ya ce: “Annabawa ne, sannan waɗanda suka fi kwatanta irin ayyukansu sannan masu biye da su. Akan jarrabi mutum gwargwadon addininsa, to idan addininsa mai ƙarfi ne sai jarrabawarsa ta fi tsananta, idan kuwa akwai sakaci a cikin addininsa sai a jarrabe shi gwargwadon ƙarfin addininsa. Jarraba ba za ta rabu da bawa ba har sai ta sanya shi yana tafiya a bayan ƙasa ba tare da wani zunubi a kansa ba.” [Tirmizi #2398 da Ahmad #1481].
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kashedi ga masu miyagun ayyuka na kafirci da saɓon Allah, masu zaton za su gagare shi, ya nuna musu cewa wannan zaton banza da wofi ne suke yi kuma mummunan hukunci suke yanke wa kawunansu, domin suna jayayya ne da ikon Allah da cikakkiyar Ƙudurarsa a kan komai.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Sanin cikakkiyar hikimar Allah wanda ya zartar da cewa ba zai ƙyale mumini ba don ya nuna imaninsa da fatar bakinsa har sai ya jarraba gaskiyar imanin nasa don ya bayyana ƙarfinsa ko rauninsa a zuciyarsa. Ta haka ne za a bambance tsakanin masu gaskiya da maƙaryata masu cika baki. Allah yakan yi jarrabawarsa ta hanyoyi daban-daban, kamar ta hanyar wadata da talauci, ko yalwa ko ƙunci ko zaman lafiya ko tashe-tashen hankula.
2. Jarrabar Allah ga muminai daɗaɗɗiyar sunnarsa ce da ta gudana a cikin al’ummun da suka gabata.
3. Abin da yake sanya wasu dogewa a kan saɓon Allah da aikata miyagun laifuka shi ne zaton da suke yi na cewa za su iya kauce wa azabar Allah. Wannan babu shakka mummunan hukunci ne da Shaiɗan ya raɗa musu.

***