2-Suratul Baƙara

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da wannan suna saboda labarin saniya da ya zo a cikinta, babu inda aka sake ba da labarinta a cikin Alƙur'ani.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Wannan Sura Madaniyya ce, watau an saukar da ita ne bayan Annabi (ﷺ) ya yi hijira zuwa Madina.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta tamanin da bakwai (87) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan 'Suratut Taɗfifi' gabanin 'Suratu Ali-Imarana'.
4. Adadin Ayoyinta:
Adadin ayoyinta a lissafin mutanen Kufa ɗari biyu da tamanin da shida ne (286). A lissafin mutanen Madina da Makka da Sham kuwa adadinsu ɗari biyu da tamanin da biyar ne (285). A wurin mutanen Basra kuwa ɗari biyu da tamanin da bakwai ne (287).
5. Falalarta:
Hakim ya ruwaito [Mustadrak 1:748] daga Abdullahi ɗan Mas'ud ya ce: “Kowane abu yana da tozo, kuma tozon Alƙur'ani shi ne ‘Suratul Baƙara’. Kuma Shaiɗan idan ya ji ana karanta ‘Suratul Baƙara’ a cikin gida sai ya fice daga gidan.” [Dubi, Al-Albani, As-Sahihah #588].
Bukhari [#5018] da Muslim [#796] kuma sun ruwaito hadisi daga Usaid bn Hudhair (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Ya Manzon Allah, jiya da daddare ina karanta Suratul Baƙara sai na ji wata ƙarar faɗuwar wani abu a bayana, sai na yi tsammani ko dokina ne ya tsinke. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ci gaba da karatunka ya baban Atiku.” Ya ce: Sai na waiwaya sai na ga kamar wata fitila ce take reto tsakanin sama da ƙasa. Manzon Allah kuwa ya ci gaba da faɗa masa: “Yi karatunka ya Baban Atiku.” Ya ce: Ya Manzo Allah, ai ban iya ci gaba da karatun nan ba. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ai waɗannan mala'iku ne waɗanda suka sauko don sauraron karatun Suratul Baƙara. Da a ce ka ci gaba da karatun da ka ga abubuwan mamaki.”
Muslim [#804] ya ruwaito daga Abu Umamatal Bahili (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Ku karanta Alƙur'ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton makarantansa. Ku karanta masu haske guda biyu, Baƙara da Suratu Ali Imran, za su zo ranar alƙiyama kamar wasu gizagizai guda biyu, ko kamar wasu ƙungiyoyi biyu na tsuntsaye masu tafiya sahu-sahu, suna jayayya don kare makarantansu. Ku karanta Suratul Baƙara, domin koyon ta albarka ne, barin ta kuma nadama ce, matsafa ba za su iya da ita ba.”
Muslim [#780] ya ruwaito hadisi daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku mayar da gidajenku kamar maƙabartu. Ku riƙa yin salla a cikinsu. Shaiɗan yana guje wa gidan da ya ji ana karanta Suratul Baƙara a cikinsa.”
6. Babbar Jigonta:
Samar da al'ummar da za ta raya bayan ƙasa da bautar Allah da riƙo da addininsa. Ta yi bayanin rarrabuwar mutane da siffofi kowane rukuni nasu, tare da bayin ginshiƙan shari'a da manya-manyan hukunce-hukuncenta.
7. Daga Cikin abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
Kasancewar wannan Sura ta sauka a lokacin da ake kafa daular Musulunci ta farko a Madina, sai ta fi ba da ƙarfi wajen kafa tarbiyyar zamantakewa tsakanin al'umma da ƙoƙarin tace ta daga dukkan wasu gurɓattattun mutane waɗanda suke ɓarna da sunan gyara. Don haka Surar ta koyar da hukunce-hukunce da dama waɗanda suka shafi rayuwar al'umma, tare da bayanin ni'imomin da Allah ya yi wa ‘yan’adam tun sanda Allah ya halicci Annabi Adamu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) Allah ya ba shi ɗaukaka ya hore masa abin da yake sama da ƙasa domin amfaninsa, tare da tunatar da shi ƙiyayyar Shaiɗan da mabiyansa a kowane zamani, waɗanda suka zaɓi su kafirce wa hanyar Allah da bin hanyar Shaiɗan, kamar Yahudu da Nasara da mushirikai.
Cikin irin waɗannan hukunce-hukunce Allah ya bayyana hukuncin ƙisasi da wasiyya da na azumi da i'itikafi da Hajji da jihadi da tsarin zamantakewar iyali da mu'amalar kuɗi da rantsuwa da sadaka da hukuncin kayan maye da hukuncin marayu da na gado da ciniki da riba da bashi da aure da hukunce-hukuncen da suka shafi mata kamar idda da saki da shayarwa da ciyarwa, da sauransu.

***

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
الٓمٓ ١ ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ ٢ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ ٣ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ وَبِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ ٤ أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ٥
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Alif Lam Mim.
2. Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taƙawa.
3. Waɗanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi.
4. Waɗanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira.
5. Waɗannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma waɗannan su ne masu samun babban rabo.

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim. Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alƙur'ani da dama da Allah ya buɗe su da irin waɗannan haruffa. Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kaɗai ya san abin da yake nufi da su. Wasu kuma sun yi ƙoƙarin bayyan ma’anonisu. Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu'ujizar Alƙurani ne ta hanyar ambaton waɗannan haruffa. Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alƙur'ani, duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su.
Allah ya siffanta wannan Alƙur’ani da cewa, babu wani kokwanto a cikinsa, wato duk abin da ya ƙunsa tabbatace ne kuma gaskiya ne, don haka ne ya zama shiriya ga masu taƙawa, yana nuna musu gaskiya da bayyana musu hukunce-hukunce wanɗanda suka shafi aƙidunsu da ibadunsu da kuma mu’amalolinsu.
An kira Alƙur'ani da sunan Littafi duk kuwa da kasancewarsa a lokacin ba a tattara shi wuri guda ba; an yi haka ne domin a yi ishara zuwa ga cewa, nan gaba za a tattara shi wuri guda ya zama littafi wanda Musulmi a kowane lokaci za su riƙa karantawa.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya fayyace siffofin masu taƙawa waɗanda Alƙur’ani yake shiryar da su. Sun siffantu da siffofi guda biyar kamar haka:
Siffa ta farko: Suna yin imani da gaibu. Gaibu shi ne duk abin da manzanni suka zo da shi, suka ba da labarinsa, kuma ido bai gan shi ba, wani tunani bai riske shi ba. Wannan ya haɗa da imani da ranar lahira da abin da ta ƙunsa na hisabi da mala’iku da labarin manzanni da littafan da Allah ya saukar gabanin zuwan Manzon Allah (ﷺ). Imani da gaibu shi ne yake bambance wa tsakanin mutum mumini da kafiri, saboda yana imani da duk wani abu da Allah ya ba da labarinsa ko Manzonsa ya faɗa ko da kuwa bai gano shi da hankalinsa ba.
Siffa ta biyu: Suna tsayar da salla, wato suna yin ta kamar yadda shari’a ta koyar da su tare da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da sharuɗɗanta.
Siffa ta uku: Suna ciyar da abin da Allah ya arzuta su da shi. Sukan fitar da zakkar dukiyoyinsu, hakanan suna sadaka ta nafila da abin da Allah ya hore musu.
Siffa ta huɗu: Su ne waɗanda suke yin imani da Alƙur’anin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (ﷺ) gaba ɗaya ba tare da ware wani ɓangare ko su riƙa karkatar da ma’anonin wani ɓangare nasa ba, kamar yadda ‘yan bidi’a suke yi ga wasu ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan bidi’o’insu da aƙidunsu. Hakanan suna yin imani da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa manzanni da annabawan da suka gabata, har da su kansu manzannin da annabawan.
Siffa ta biyar: Su ne waɗanda suka tabbatar da zuwan ranar tashin alƙiyama da abubuwan da za ta zo da su na tayar da matattu da yi musu hisabi da saka wa mutanen ƙwarai da Aljanna; masu miyagun laifuffuka kuwa a saka musu da wutar Jahannama. An ware batun imani da ranar lahira duk kuwa da cewa ya shiga cikin batun imani da gaibu, saboda a zaburar da mutane ga ayyukan alheri a kuma tsoratar da su game da munanan ayyuka.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya faɗi sakamakon masu waɗannan siffofi da cewa, suna kan wata shiriya mai girma daga Allah mai yi musu tarbiya ta ƙwarai. Domin babu wata shiriya da ta kai siffantuwa da waɗannan siffofi. Don haka su ne waɗannan suke da babban rabo daga Allah, wato samun yardar Allah da gidan Aljanna ranar gobe alƙiyama.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Girman mu'ujizar Alƙur'ani.
2. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi ishara zuwa ga cewa, za a tattara Alƙur'ni wuri guda don ya zama littafin da Musulmi za su riƙa ɗauka suna karantawa a kowane zamani.
3. Alƙur'ani shiriya ne ga mutune masu taƙawa, watau masu kiyaye dokokin Allah. Gwardon taƙawar bawa gwargwadon yadda zai dace da shiriyar Alƙur'ani. Wanda kuma ya rungume shi yana aiki da shi to babu shakka shiriyarsa za ta riƙa hauhawa tana ƙaruwa.
4. Duk abin da Alƙur’ani ya ƙunsa gaskiya ne babu kokwanto ko kaɗan a cikinsa.
5. Falalar yin imani da gaibu, domin shi ne abin da yake buƙatar ƙarfin imani, saɓanin abin da kowa yake iya gani ko yake iya ji, wannan abu ne da babu mai iya musunta samuwarsa.
6. Girman sha'anin tsai da salla, domin ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan Musulunci.
7. Falalar ciyar da dukiya don Allah.
8. Siffar masu taƙawa ta ƙunshi bauta wa mahalicci da kyautata wa mahaluki.
9. Imani da duk littattafan da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar wa manzanninsa, domin sanin cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) bai bar bayinsa hakanan sakaka ba tare da bayyana musu hanyar shiriya ba.
10. Shiriya da rabauta ba za su taɓa samuwa ga bawa ba har sai ya rungumi wannan hanyar, ya kuma siffantu da waɗannan siffofi.

***