19-Suratu Maryam

Mabuɗin Surar:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da sunan ‘Suratu Maryam’. Kuma wannan shi ne sunanta a cikin Mus'hafai da littattafan Tafsiri da na Hadisi. Abin da ya sa aka kira ta da wannan suna kuwa, saboda a cikinta an yi faffaɗar magana a kan ƙissar Maryamu, tare da batun ɗanta Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi), da kuma na danginta. A gabanin saukar da wannan Sura babu wata Sura da aka yi batun Nana Maryam da ɗanta Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) kamar yadda aka yi a wannan Sura. Sai daga baya Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi batunta a cikin Suratu Ali Imran.
A cikin wasu littattafan Hadisi an kira ta da sunan haruffanta na farko, watau () kamar yadda ya zo a cikin hadisin Ummu Salama wanda ya yi magana a kan hijirar Musulmi zuwa ƙasar Habasha, inda take cewa: “Sai Ja’afar ya karanta ()”. [Ahmad #1740].
Abu Huraira da Ibn Abbas sun kira ta da haka. [Dubi, Musnad #8552 da Ibnu Hibban #7156 da Tafsirin Ibnu Ashur, Juzu’i na 8, shafi na 58].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Sura ce Makkiyya a wajen baki ɗayan malamai. Amma an rawaito daga Muƙatil ɗan Sulaiman ya ce: “Ayar sujjada, watau aya ta (58) Madaniyya ce”.
Suyuɗi a cikin littafin “Al-Itaƙaan” ya hakaito cewa wani ya togace aya ta (71) ya ce Madaniyya ce, amma kuma bai ambaci sunansa ba. Magana dai ingantacciya ita ce wannan Surar gaba ɗayanta Makkiyya ce.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce sura ta arba’in da huɗu (44) a jerin saukar surori. An saukar da ita bayan ‘Suratu Faɗir’ kafin ‘Suratu `Ɗaha’.
4. Adadin Ayoyinta:
A lissafin mutanen Makka da Madina ayoyinta tis’in da tara ne (99), amma a lissafin mutanen Sham da Kufa kuwa adadinsu tis’in da takwas ne (98). Wannan shi ne kuma abin da yake rubuce cikin Mus'hafai.
5. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Kaɗaita Allah da bauta tare da kore masa abokin tarayya, da kuma kore masa ɗa.
• Ta taɓo batun tashin alƙiyama, inda ta hasko wasu abubuwa da za su gudana a ranar.
• Tubalin ginin wannan Surar ƙissoshi ne waɗanda suka fara da ƙissar Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Yahya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan ƙissar Maryamu da haihuwar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan kuma wani ɓangare na ƙissar Annabi Ibrahimu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mahaifinsa. Sannan ta yi nuni zuwa ga wasu annabawa, kamar Annabi Musa da Annabi Is’haƙa da Annabi Isma’ila da Annabi Idris. A taƙaice ana iya cewa, kimanin biyu bisa ukunta (2/3) ƙissoshi ne.
• Ta yi nuni zuwa ga girman sha’anin Alƙur’ani.
• Cikin manya-manyan manufofin wannan Sura akwai tabbatar da yalwar rahamar Ubangiji, domin an ambaci “Arrahman” a cikinta har sau goma sha shida (16), wanda hakan ke tabbatar da cewa sunan Allah ne, kuma Rahama Siffarsa ce, don kuma wannan ya zama martani ga mushrikan Makka da suke cewa su ba su yarda da wannan suna ba

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
كٓهيعٓصٓ ١ ذِكۡرُ رَحۡمَتِ رَبِّكَ عَبۡدَهُۥ زَكَرِيَّآ ٢ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيّٗا ٣ قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ ٱلۡعَظۡمُ مِنِّي وَٱشۡتَعَلَ ٱلرَّأۡسُ شَيۡبٗا وَلَمۡ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيّٗا ٤ وَإِنِّي خِفۡتُ ٱلۡمَوَٰلِيَ مِن وَرَآءِي وَكَانَتِ ٱمۡرَأَتِي عَاقِرٗا فَهَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا ٥ يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنۡ ءَالِ يَعۡقُوبَۖ وَٱجۡعَلۡهُ رَبِّ رَضِيّٗا ٦
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. KAF HA YA AIN SAD
2. (Wannan) ambaton rahamar Ubangijinka ne (da Ya yi wa) Bawansa Zakariyya.
3. Lokacin da ya kira Ubangijinsa (ya roƙe Shi) cikin asiri.
4. Ya ce: “Ya Ubangiji lalle ƙasusuwana sun yi rauni, kaina kuma ya yi fari fat da furfura, Ubangijina ban kuma zama mai taɓewa ba game da roƙon Ka.
5. “Kuma lalle ni na ji tsoron dangina a bayana, matata kuma ga ta bakarara ce, saboda haka Ka yi mini baiwa daga gare Ka ta (ɗa) majiɓinci.
6. “(Wanda) zai gaje ni ya kuma gaji iyalan Ya'aƙub; Ubangijina kuma Ka sanya shi yardajje (a wurinka).”

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa kamar yadda ya buɗe wasu surori da suka gabace ta. Mun riga mun ambaci bayanin malamai a kansu. [Dubi farkon Suratul Baƙara].
Allah (Mai tsarki da daukaka) a nan yana ba da labarin bawansa ne Annabi Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) game da wata babbar rahama da ya yi masa ta samun haihuwa bayan ya tsufa tukuf bai haihu ba.
Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ɗaya ne daga cikin annabawan Banu Isra’ila, yana auren `yar’uwar Maryam (() mahaifiyar Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi).
An karɓo daga Maliku ɗan Sa’asa’a (Allah ya kara masa yarda) a cikin dogon hadisinsa na bayanin Isra’in Annabi (ﷺ) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Sai Jibrilu ya hau da shi har suka iso sama ta biyu, sai ya nemi a buɗe ƙofa, sai aka ce masa: “Wane ne?” Sai ya ce: “Jibrilu ne.” Sai aka ce masa: “Wane ne kuma tare da kai?” Sai ya ce: “Muhammadu ne.” Sai aka ce: “Shin an aika masa ne?” Ya ce: “E.” Ko da na shiga sai na ga Yahya da Isa kuma su biyun ‘ya’yan mata zar suke...” [Dubi Bukhari #3430].
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi addu’a cikin dare a ɓoye ya roƙi Allah ya ba shi ɗa. Ya nuna wa Ubangijinsa raunin jikinsa saboda tsufa, ga shi kuma furfura duk ta baibaye kansa, kuma ya tabbata ba zai rasa samun biyan buƙatarsa ta samun ɗa ba duk da halin da yake ciki.
Sai kuma ya bayyana dalilinsa na neman haihuwa a wannan yanayi, shi ne yana jin tsoron bayan mutuwarsa danginsa ba za su tsaya su kula da tafiyar da harkokin addini ba kamar yadda yake yi a matsayinsa na Shugaban Limaman Banu Isra’ila a zamaninsa, domin ganin yadda suka shagaltar da kansu da harkokin neman abinci. Ya kuma bayyana cewa matarsa bakarara ce ba ta haihuwa; wannan ya sa yake ta roƙon Allah ya dube shi da rahamarsa ya ba shi ɗa wanda zai taimaka masa, wanda kuma zai gaji annabta da ilimi daga gare shi da kuma iyalan Ya'aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Sannan ya roƙi Allah ya sanya shi ya zama yardadde a addininsa da halayensa da iliminsa a wajensa da wajen sauran jama’a.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Zamantowar mutum bawan Allah, watau mai bauta gare shi tare da so da ƙanƙantar da kai, matsayi ne a wurin Allah da yakan jawo masa samun rahamarsa a duniya da lahira.
2. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana son bawansa ya roƙe shi yana mai ikhlasi cikin addu’arsa. Don haka Zakariyya (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fifita ya yi addu’arsa a ɓoye ba tare da wani ya sani ba.
3. Bawa ya bayyana rauninsa da gajiyawarsa yana daga cikin abin neman kusanci zuwa ga Allah, domin ya amsa masa addu’arsa.
4. Yana da kyau mai addu’a ya ambaci ni’imomin da Allah ya yi masa ya yi tawassuli watau ya nemi kusanci da shi da hakan.
5. Nuna damuwa da masalaha ta addini fiye da sauran maslahohi.
6. Annabawa suna barin gadon ilimin annabci ne ba na dukiya ba, shi ya sa Zakariyya ya roƙi Allah ya ba shi ɗa don ya gaji iliminsa da na zurriyyar gidan Annabi Ya'aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi). Wannan ya nuna ba gadon dukiya ne ba, domin gadon dukiyar zurriyyar Ya'aƙubu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) tana ga magadansu ne ba ɗan Zakariyya ba.

***