18-Suratul Kahf
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Ana kiran ta ‘Suratul Kahf’ domin a cikinta ne labarin ‘As’habul Kahfi ’ ya zo, wato labarin mutanen Kogo. Duk ilahirin Alƙur’ani babu inda aka ba da labarinsu sai a wannan Sura kaɗai, shi ne dalilin da ya sa ta ci sunansu.
Kiran wannan Sura da wannan sunan ya zo a cikin ingantattun hadisai na Annabi (ﷺ), kuma shi ne abin da ke rubuce cikin mushafai.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Ibnu Aɗiyya ya kawo cewa, malaman Tafsiri sun haɗu a kan cewa wannan Sura ce Makkiyya. Abu Abdullahi Al- Ƙurɗubi ya goyi bayansa a kan haka.
Amma wasu malamai sun togace aya ta (1) zuwa ta (8) sun ce a Madina aka saukar da su. Wasu kuma suka togace aya ta (28). To amma ingantacciyar magana ita ce, wannan Sura daga farkonta har ƙarshenta Makkiyya ce.
3. Jerin Saukarta:
Wannan Sura ita ce ta sittin da takwas (68) a jerin saukar surorin Alƙur’ani. Ta sauka bayan ‘Suratul Gashiya’, kafin saukar ‘Suratus-Shura’.
4. Adadin Ayoyinta:
A lissafin mutanen Makka da Madina ayoyinta ɗari da biyar ne (105). A lissasfin mutanen Sham kuwa ayoyinta ɗari da shida ne (106). Su kuma mutanen Basra a lissafinsu ɗari da goma sha ɗaya ne (111). Mutanen Kufa kuwa a wurinsu ayoyinta ɗari da goma ne daidai (110). Watau dai an samu saɓani ne wajen tantance farkon wasu ayoyi da ƙarshensu, wasu sai su lissafa aya biyu a matsayin ɗaya, wasu kuma su lissafa aya ɗaya a matsayin biyu.
5. Sababin Saukarta:
Imam Ibnu Jarir ya ruwaito da isnadinsa daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) cewa: “Yayin da Larabawan Ƙuraishawa suka ga irin yadda Annabi (ﷺ) yake matsa musu da kira zuwa ga imani da Allah, da jan hankalinsu a kan su bi Alƙur’ani, sai suka tura wakilansu Madina wurin Yahudawa domin su yi musu tambaya a kan Annabi (ﷺ) don su ba su wani bayani wanda za su ƙure Annabi (ﷺ) da shi, domin su ma Yahudawa an saukar musu da littafi suna da ilimi. Da suka je sai Yahudawa suka ce musu su koma su yi wa Annabi (ﷺ) tambayoyi uku; idan ya ba su amsarsu daidai, to tabbas shi Annabi ne sai su bi shi; idan kuwa ya kasa ba da amsarsu, to shi ba annabin gaskiya ba ne, daga nan sai su yanke shawarar abin da ya kamata su yi masa. Suka umarce su da su tambaye shi ƙissar As’habul Kahfi, da ta Zulƙarnaini, da kuma sha’anin Ruhi, watau rai da yake jikin ɗan’adam.
Waɗannan wakilai suka dawo Makka suka kuma yi wa Annabi (ﷺ) waɗannan tambayoyi, sai ya nemi cewa, su dawo gobe zai ba su amsa. Sai ya manta bai ce insha Allahu ba, saboda haka sai aka samu jinkirin saukar wahayi na kimanin kwana goma sha biyar. Wannan kuwa ya sa Annabi (ﷺ) ya shiga matuƙar damuwa, kuma aka yi ta yayata maganganu a cikin garin Makka cewa, aljanin da yake kawo wa Annabi (ﷺ) labarai shi ma ya watsar da shi. Daga baya Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar masa da wannan Sura, wadda a cikinta ya ba shi tarbiyyar cewa, kada ya sake cewa zai yi wani abu gobe ba tare da ya haɗa da insha Allahu ba”.
Wannan ruwaya mai rauni ce, a cikin sanadinta akwai mai ruwayan da ba a bayyana kowane ne shi ba. Amma duk da haka wasu malaman sukan ambaci wannan ƙissar.
6. Falalar Surar:
Hadisai ingantattu sun tabbata daga Annabi (ﷺ) game da falalar karanta Suratul Kahfi:
An karɓo daga Albara’u ɗan Azib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani mutum yana karanta Suratul Kahfi a cikin gidansa, a lokacin kuwa dokinsa yana ɗaure, sai ya riƙa zabura yana firgita. Da ya fito domin ya ga abin da yake faruwa, sai ya ga wani girgije ne ya yiwo ƙasa-ƙasa ya lulluɓe nahiyar gidansa. Washe-gari ya je ya faɗa wa Annabi (ﷺ) abin da ya faru, sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Ka ci gaba da karatunka wane, domin wannan natsuwa ce take sauka domin karatun Alƙur’ani.” [Bukhari #3614 da Muslim #795].
Wannan mutum shi ne Usaidu ɗan Hudhair, kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi.
An karɓo daga Abud-Darda’i (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) yana cewa: “Duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahfi to za a tsare shi daga fitinar Dujal.” [Muslim #809].
A wani lafazin kuma: “Ayoyi goma na ƙarshe na Suratul Kahfi”. Amma lafazin farko shi ne ya inganta. [Duba Ibnul Ƙayyim, Jala’ul Afham, shafi na 325].
Watau idan Dujal ya bayyana to shi mutumen zai samu kariya a dalilin waɗannan ayoyi guda goma da ya haddace.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa:
• Wannan Sura ta sauka a Makka daidai lokacin da ake nuna wa Annabi (ﷺ) da sahabbansa tsananin ƙiyayya da gaba, har wasu daga cikinsu suka yi gudun hijira zuwa Habasha. Ana cikin irin wannan yanayi wannan Surar ta sauka, domin ta karantar da Annabi (ﷺ) da sahabbansa cewa, su yi haƙuri, haka sha’anin addini ya gada. Allah Ta’ala kuma ya halicci rayuwa ne gaba ɗaya don ya jarraba ɗan’adam ya ga wane ne zai tsaya ya kyautata aikinsa.
• Surar ta kuma ba da misali na wasu da suka tsinci kawunansu cikin fitina amma suka riƙe Allah suka dogara gare shi, kuma ya kuɓutar da su daga wannan fitinar. Su ne As’habul Kahfi waɗanda suka taso a garin da ba imani a cikinsa, amma Allah Ta’ala ya sa duk da haka suka iya rinjayar zukatansu, suka kuma rinjayi fitinar da suka samu kawunansu a ciki, Allah ya ba su nasara ya tsare su.
• A wannan Sura, Allah Ta’ala ya lallashi Annabi (ﷺ) yayin da ya shiga damuwa dangane da mutanensa da suka ƙi amsar gaskiyar da ya zo musu da ita, ya nuna masa kada ya damu, domin ya halicci mutane ne daban-daban, kuma ya yi su don ya jarraba su, a cikin su akwai wanda zai ci jarrabawar, akwai kuma wanda ba zai ci ba. Don haka waɗanda Allah ya ga dama ya shiryar daga cikinsu za su shiriya kamar yadda ya shiryar da samarin As’habul Kahfi.
• Haka kuma Surar ta yi bayanin yadda Iblis ya nuna wa mutum na farko ƙiyayya shi da zurriyyarsa. Ta bayyana cewa duk wani ruɗi na duniya da yaudarar ƙyale-ƙyalenta daga Shaiɗan ne, don haka mutane kada su bari ya ruɗe su ya hana su samun rabauta ta duniya da lahira.
• Surar ta zo da faɗakarwa dangane da wanda zai ruɗu da iliminsa, inda ta tarbiyyanci mutane a kan su san cewa, duk inda mutum ya kai ga ilimi to ilimin Allah ya fi nasa, Allah kuma zai iya sanya abin da bai sani ba a hannun wani na ƙasa da shi, kamar yadda ƙissar Annabi Musa da Khadir ta nuna.
• Surar ta ja hankali a kan wanda zai ruɗu don Allah ya mallaka masa wani mulki na duniya, har ya kai shi ga bijire wa Allah, ko ya kai shi ga zalunci a bayan ƙasa. Ƙissar Zulƙarnaini ta bayyana mana wannan. Duk da ɗimbin ilimi da mulki da Allah ya ba shi, ya shiga lunguna-lunguna na duniya da ƙarfin ikonsa, amma hakan bai sa ya zalunci wani ba, hakan kuma bai sa shi ya bijire wa Allah ba. Ya yi amfani da ƙarfn mulkin da Allah ya ba shi wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
• Surar dai ta zo da misalai na wasu abubuwa kishiyoyin juna. Ta yi bayanin alhairi, ta kuma yi bayanin sharri; ta yi bayanin imani, kuma ta yi bayanin kafirci; ta yi bayanin adalci, ta kuma yi bayanin zalunci; haka kuma ta yi bayanin waɗanda suka yi imani, Allah kuma ya ƙara musu shiriya, da kuma waɗanda suka kafirce wa Allah. Wannan duka don ta ɗora mutum a kan tarbiyyar da za ta sanya shi ya ci jarrabawar da Allah ya shirya masa.
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya saukar wa da Bawansa Littafi, bai kuma sanya masa wata karkata ba.
2. Daidaitacce ne, don ya yi gargaɗi game da azaba mai tsanani daga gare Shi (wato Allah), ya kuma yi wa muminai waɗanda suke aiki nagari albishir cewa suna da lada kyakkyawa.
3. Madawwama a cikinsa har abada.
4. Ya kuma gargaɗi waɗanda suka ce Allah Yana da ɗa.
5. Ba su da wani ilimi game da shi (wannan zance) kuma iyayensu ma ba su da (ilimi game da shi). Kalmar da take fitowa daga bakunansu ta yi girma. Ba abin da suke faɗa sai ƙarya.
6. To ko mai yiwuwa ne za ka kashe kanka da baƙin ciki, in ba su yi imani da wannan zancen ba (watau Alƙur'ani).
7. Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan ƙasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?
8. Lalle kuma Mu za Mu mai da abin da yake kanta (ya zama) turɓaya ƙeƙasasshiya.
A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da godiya da yabo da kirari ga Zatinsa don ya tabbatar da cewa, shi ne ya fi kowa cancantar duk wata sifa ta ɗaukaka da kamala. Ya bayyana cewa, shi ne wanda ya saukar wa da bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) Alƙur’ani wanda ba shi da wata tawaya ta kowace fuska. Ya sanya shi littafi ne daidaitacce wanda babu tufka-da-warwara a cikinsa domin ya tsoratar da kafirai da shi game da wata azaba mai tsanani daga Allah da take jiran su a lahira idan ba su yi imani da Allah da Manzonsa ba. Hakanan kuma ya yi wa muminai waɗanda suka yi ayyuka na ƙwarai albishirin samun wani kyakkyawan sakamako da babu kamarsa, wanda shi ne gidan Aljanna. Za su zauna har abada a cikin wannan sakamako ba zai yanke musu ba.
Sannan kuma ya gargaɗi kafirai waɗanda suke cewa Allah (Mai tsarki da daukaka) yana da ɗa, su ne Yahudu da Nasara har ma da mushirikan Larabawa masu cewa mala’iku ‘ya’yan Allah ne mata. Ya bayyana cewa masu irin wannan ƙagen ga Allah ba su da wani ilimi ko wani dalili da suka dogara da shi a kan da’awarsu. Kai har ma iyayensu da suke koyi da su ba su da wani ilimi a kan wannan lamari da suke da’awa. Allah ya bayyana cewa, magana mummuna da take fitowa daga bakunansu ta yi matuƙar muni. Ba komai suke furtawa ba kuma sai ƙarya zunzurutunta.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da lallashin Manzonsa (ﷺ) wanda rashin yin imanin kafirai yake matuƙar damunsa. Ya nuna masa cewa, kada ya kashe kansa da yawan damuwa da yake sakawa a ransa don mutanensa sun ƙi yin imani da Alƙur’ani, domin shiriyarsu ba a hannunsa take ba.
Sai kuma ya bayyana masa cewa, duk wani abu da ya halitta a doron ƙasa ya yi shi ne don jarrabawa don ya tantance waɗanda suka fi kyakkyawan aiki daga cikin bayinsa. Kuma daga ƙarshe duk wani ƙyale-ƙyale da yake bayan ƙasa zai mayar da shi turɓaya ƙeƙasasshiya wadda babu wani tsiro a kanta. Don haka ya daina damuwa da abin da zai gani ko zai ji daga maƙiyansa domin kowa daga ƙarshe zai koma ne ga Allah ya yi wa kowa hisabi a kan abin da ya aikata.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yabi kansa bisa ga saukar da Alƙur’ani ga bawansa Annabi Muhammadu (ﷺ) domin shi ne mafi girman ni’imar da ya yi wa mutane a wannan duniya, domin da shi ne ya fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma shi ne sababin samun tsirarsu a duniya da lahira.
2. Kiran Alƙur’ani da sunan 'Littafi' yana ishara zuwa ga yadda zai zamanto daga ƙarshe, watau za a tattara shi wuri guda a matsayin littafi ɗaya bayan a da yana rubuce ne a cikin wasu abubuwan rubutu daban-daban a wajen sahabbai.
3. Alƙur’ani cikakken littafi ne kuma ingantacce, babu wata tawaya ko saɓani a cikinsa. Duk hukunce-hukuncensa adalci ne, labaran cikinsa kuwa duka gaskiya ne.
4. Babbar manufar saukar da Alƙur’ani ita ce don a yi wa’azi da shi ta hanyar albishir da kuma gargaɗi.
5. Duk masu da’awar Allah (Mai tsarki da daukaka) yana da ɗa ba su da wani dalili daga Allah ko na hankali sai dai shaci-faɗi kawai.
6. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya jera matakai uku wajen rushe da’awar masu riya cewa yana da ɗa, ya fara da mafi sauƙin muni har ya zuwa mafi tsananin munin.
Na farko, ya bayyana cewa ba su da wani ilimi a kan haka su da iyayensu. Yin magana ba bisa ilimi ba kuwa ba shakka mummunan abu ne.
Na biyu, ya tabbatar musu da cewa wannan magana da suke furtawa ta kai matuƙa ga muni.
Na uku, ya bayyana musu cewa maganarsu ƙarya ce zunzurutunta babu gaskiya ko kaɗan a cikinta.
7. Tsananin tausayin Annabi (ﷺ) ga al’ummarsa, don haka ya riƙa shiga cikin matsananciyar damuwa a kan rashin ba da gaskiyarsu, har sai da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tausaya masa.
8. Duk wani mai kira zuwa ga Allah wajibin da yake kansa shi ne ya yi matuƙar ƙoƙarinsa wajen isar da gaskiya ga mutane da yi musu bayanin hanyar ɓata don su nisance ta. Idan sun shiryu to wannan abin faranta rai ne; idan kuwa sun ci gaba da zama cikin ɓatansu to kada ya saka kansa cikin damuwa da ɓacin rai wanda har zai sa shi ya yi rauni, gwiwarsa ta yi sanyi ya kasa ci gaba da aikinsa na da’awa.
9. Allah ya bayyana cewa duk wani ƙyale-ƙyale a bayan ƙasa na kayan ciye-ciye ko na shaye-shaye ko na tufafi ko wuraren zama ko abubuwan hawa da sauransu, duk wannan jarrabawa ce ta duniya domin a tantance waɗanda suka fi kyautata ayyukansu ga Allah (Mai tsarki da daukaka).