12-Suratu Yusuf

Mabuɗin Surar:
1. Sunanta:
Ana kiran ta da suna “Suratu Yusuf” saboda ta ƙunshi labarin Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) gaba ɗaya. Babu wata sura da ta zo da labarinsa daki-daki in ban da wannan Surar. Ba a kuma ambaci sunansa a ko’ina ba sai a nan da kuma cikin “Suratul An’am” da “Suratu Ghafir”.
An Karɓo daga Uƙbatu ɗan Amiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ce wa Manzon Allah (ﷺ) ya karanta mini Suratu Hud da Yusuf….”. [Ahmad#17418, Nasa’i#953].
An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na kasance a garin Himsu (cikin ƙasar Syria), sai wasu suka roke ni in karanta musu Alƙur’ani, sai na karanta musu Suratu Yusuf”. [Bukhari#5001 da Muslim#801].
Ya zo a hadisin Amru ɗan Maimunu da yake ba da labarin kashe Sayyiduna Umar, yana cewa: “Umar ya kasance idan ya wuce ta tsakanin sahu biyu (na masallata) sai ya ce: “Ku daidaita sahu”, sai ya tabbata babu wani bigire tsakanin sahu da sahu sannan sai ya wuce gaba ya yi kabbarar harama. Wani lokaci sai ya karanta Suratu Yusuf ko kuma ya karanta Suratun Nahl, ko makamancin haka a raka’ar farko” watau a sallar Asuba. [Bukhari#3700].
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Malamai sun haɗu a kan cewa, Sura ce Makiyya.
3. Jerin Saukarta:
An saukar da ita bayan Suratu Hud. Ta kuma sauka ne a dunƙule a lokaci guda.
4. Adadin Ayoyinta:
Tana da ayoyi ɗari da goma sha ɗaya (111).
5. Babban Jigonta:
• Bayani a kan cewa kyakkyawan ƙarshe yana tabbata ne ga masu tsoron Allah da haƙuri, komai runtsi da wahalhalun rayuwa.
>>>>>>>>• Lallashin Annabi (ﷺ) da sahabbansa da kwantar musu da hankali.
6. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
Ita ce surar da ta zo da ambaton ƙissar Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a dunƙule a wuri guda. Babu wata ƙissa da ta zo kamar haka a cikin Alƙur’ani sai wannan ƙissar ita kaɗai.
Daga fittattun abubuwan da ta ƙunsa kuwa sun haɗa da:
• Faɗar wata falala ta Alƙur’ani wajen ba da labari cikin salo mai cike da hikima da jan hankali.
• Bayanin mafarkin Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da makircin da ‘yan’uwansa suka ƙulla masa da hassadar da suka nuna masa.
• Yadda ayarin matafiya suka tsinci Annabi Yusufu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a kururramar rijiya sannan suka sayar da shi a Masar; da makircin da ya gamu da shi daga matar Azizu da wasu daga cikin matan Masar.
• Shigarsa kurkuku duk da cewa ya tabbata ba shi da wani laifi da yadda ya zama mai kira zuwa ga Allah a cikin kurkukun.
• Mafarkin Sarkin Masar da fassarar da Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mafarkinsa da wanke shi daga zargin matar Azizu da fitowarsa daga kurkuku da karɓar aikin mai kula da taskokin arzikin ƙasa da yadda Allah ya ɗaukaka sha’aninsa.
• Haɗuwar Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘yan’uwansa ba tare da sun gane shi ne Yusuf ba, da yadda ya nemi idan sun tashi dawowa Masar su zo tare da ɗan’uwansa da kuma bayanin yadda Allah ya shirya masa dabarar riƙe ɗan’uwansa, sai kuma bayanin abin da ya biyo bayan haka na faɗawar mahaifinsu cikin baƙin ciki da tashin hankali.
• Haɗuwar Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ‘yan’uwansa da yadda ya bayyana musu kansa, ya kuma tuna musu abin da suka aikata a gare shi tare da yi musu afuwa, sannnan kuma da yadda ya umarce su su koma wajen babansu su jefa masa rigar Annabi Yusufu a fuskarsa domin ganinsa ya dawo masa.
• Zuwansu Masar gaba ɗaya tare da mahaifinsu da karramawar da Annabi Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi wa mahaifansa da ‘yan’uwansa.
• Ɗauraya da ta biyo bayan ƙissar Yusuf (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) a inda Allah ya bayyana abin da yake nuna cewa Alƙur’ani daga wajensa yake da abin da yake ƙara tabbatar da gaskiyar Annabi Muhammadu (ﷺ), ya kuma yi bayanin aikin Annabi (ﷺ) da matakin da mushirikai suka ɗauka game da da’awarsa, tare da tabbatar da cewa, Annabi (ﷺ) ba shi ne farau a cikin manzanni ba, sannan kyakkyawan ƙarshe nasa ne shi da mabiyansa muminai.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ ١ إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ ٢ نَحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ أَحۡسَنَ ٱلۡقَصَصِ بِمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ ٣
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. ALIF LAM RA. Waɗannan ayoyi ne na Littafi mabayyani.
2. Lalle Mu Muka saukar da shi Alƙur’ani da (harshen) Larabci don ku hankalta.
3. Mu ne Muke labarta maka (labari) mafi kyan labartawa ta hanyar yi maka wahayin wannan Alƙur’ani, ko da yake gabaninsa kana cikin marasa sanin(sa).

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da wasu haruffa kamar yadda ya yi a wasu surori da suka gabata. Babbar hikimar da aka ambata game da waɗannan haruffa ita ce, Allah yana nuni ne da su zuwa ga mu’ujizar Alƙur’ani wanda duk masu fasahar Larabawa suka kasa kawo irinsa duk kuwa da cewa suna magana da irin haruffan da Alƙur’ani ya sauka da su. Wannan yana ƙara tabbatar da cewa Alƙur’ani maganar Allah ce ba ta wani ba.
Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa Manzonsa cewa, waɗannan ayoyi da aka saukar cikin wannan Sura suna cikin bayyanannun ayoyin da wannan littafi na Alƙur’ani ya ƙunsa.
Sai kuma ya bayyana wa Manzonsa cewa, shi ne ya saukar da Alƙur’ani cikin harshen Larabci domin Larabawa da sauran masu jin wannan harshe su fahimci ma’anonin da ya ƙunsa.
Sai kuma ya faɗa masa cewa, shi ne zai ba shi mafi kyan labarai domin ingancinsu da kyakkyawan zubin salonsu da tsarinsu da sauƙin fahimtarsu, ta hanyar saukar masa da Alƙur’ani wanda littafi ne da babu kamarsa. Sai kuma ya tabbatar wa Manzon Allah (ﷺ) cewa, kafin ya saukar masa da wannan littafin yana cikin waɗanda ba su san komai ba game da shari’o’i da kuma ƙissoshin da ya ƙunsa.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Tabbatar da mu’ujizar Alƙur’ani.
2. Muhimmancin koyon harshen Larabci da darajarsa, saboda shi ne harshen da aka saukar da mafificin littafi da shi, watau Alƙur’ani.
3. Babu masu fahimtar Alƙur’ani sai masu hankali.
4. Labaran da Alƙur’ani ya zo da su sun fi kowane irin labarai kyau da inganci, saboda gaskiyar da ke cikinsu da salo da azanci mai ƙayatarwa.
5. Kafin saukar da Alƙur’ani, Annabi (ﷺ) bai san komai na shari’a da ƙissoshin annabawa ba.
6. Tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi (ﷺ).