112-Suratul Ikhlas
Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura ta shahara da suna ‘Suratul Ikhlas’, amma abin da ya zo a cikin hadisan Manzon Allah (ﷺ) da maganganun sahabbai an kira ta ‘Suratu Ƙul Huwallahu Ahad’.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Yawancin malamai suna ganin Sura ce Makkiyya, wasu kuma kaɗan sun ce Madaniyya ce.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta ashirin da biyu (22) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratun Nasi’ gabanin ‘Suratun Najmi’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta huɗu ne (4) a wurin mutanen Madina da Kufa da Basra. Amma a wajen mutanen Makka da Sham ayoyinta biyar ne (5).
5. Falalarta:
An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani ya ji wani mutum yana ta maimaita karatun ‘Ƙul Huwallahu Ahad’, da gari ya waye sai ya je wajen Annabi (ﷺ) ya faɗa masa abin da ya ji, watau kamar ya raina karatun mutumin, sai Manzo Allah (ﷺ) ya ce masa: “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lalle ita wannan Sura tana daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur’ani.” [Bukhari #7374].
An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Annabi (ﷺ) ya shugabantar da wani mutum a kan wata runduna, sai yake jan mutanensa salla, yana cike karatunsa da ‘Ƙul Huwallahu Ahad’, da suka dawo sai suka faɗa wa Annabi (ﷺ) abin da mutumin nan ya riƙa yi musu. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku tambaye shi, me ya sa yake yin haka?” Sai suka tambaye shi, sai ya ce: “Saboda ita siffar Allah mai rahama ce, kuma ni ina son in riƙa karanta ta.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku ba shi labari cewa, lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) yana son shi.” [Bukhari #7575 da Muslim #813].
6. Babban Jigonta:
Tana tabbatar da cikar Uluhiyyar Allah da tsarkakarsa daga duk wani aibi ko tawaya.
7. Daga Cikin Abubuwan Da Ta Ƙunsa Akwai:
• Tabbatar da Ɗayantakar Allah (Mai tsarki da daukaka).
• Tabbatar da cikar Wadatuwarsa da Zatinsa, kuma babu wanda ake nufa da buƙata sai shi kaɗai.
• Rushe aƙidar jingina wa Allah haihuwar ɗa ko kini.
***
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka ce: “Shi ne Allah Ɗaya.
2. “Allah Abin nufa da buƙatu.
3. “Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba.
4. “Kuma babu wani da ya kasance kini a gare Shi.”
Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya furta cewa, lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) Ɗaya ne, ya kaɗaita da cancantar a bauta masa, babu wani abin bauta sai shi kaɗai. Shi ne kuma abin nufa da buƙata, wanda shugabanci ya tuƙe zuwa gare shi, domin ya tattara duk siffofin kalama da ɗaukaka.
Yana daga cikin kamalarsa cewa, shi bai haifi komai ba, ba kuma wanda ya haife shi, don haka ba shi da ɗa ba shi da mahaifi. Sannan kuma babu wani ɗaya cikin halittunsa da ya zamanto kini a gare shi, domin babu mai kama da shi a sunayensa da siffofinsa da ayyukansa.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Tabbatar da Ɗayantakar Allah (Mai tsarki da daukaka) cikin Uluhiyyarsa da Rububiyyarsa da sunayensa da siffofinsa.
2. Duk wani girma da ɗaukaka sun tuƙe ga Allah (Mai tsarki da daukaka), shi ne wanda kowa da komai suke da buƙata a wurinsa, amma shi ba ya da buƙata a wurin kowa.
3. Tsarkake Allah daga haihuwa, watau shi bai haifi kowa ba, kuma ba wanda ya haife shi. Don haka duk wanda ya jingina haihuwar ɗa namiji ko mace ga Allah, to lalle ya ɓata ɓata mai nisa.
4. Allah (Mai tsarki da daukaka) bai yi kama da kowa ba cikin halittunsa, kuma shi kaɗai ne ba ya da kini.
5. Wannan Surar ta ƙunshi Tauhidin sunayen Allah da siffofinsa.