109-Suratul Kafirun

Mabuɗin Sura:
1. Sunanta:
Wannan Sura ta shahara da ‘Suratul Kafirun’. A Sahihul Bukhari an kira ta da ‘Suratu Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’, hakanan aka ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas da Abdullahi ɗan Zubair (().
2. Sanda Aka Saukar Da Ita:
Sura ce Makkiyya.
3. Jerin Saukarta:
Ita ce Sura ta goma sha takwas (18) a jerin saukar surorin Alƙur’ani, ta sauka bayan ‘Suratul Ma’un’ kafin ‘Suratul Fil’.
4. Adadin Ayoyinta:
Ayoyinta shida ne (6).
5. Falalarta:
• An karɓo daga wani dattijo da ya yi zamani da Annabi (ﷺ) ya ce: Na fita wata tafiya tare da Manzon Allah (ﷺ) sai ya wuce ta gaban wani mutum yana karanta ‘Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’, sai ya ce: “Amma dai wannan haƙiƙa ya kuɓuta daga shirka.” Sai ya ga wani kuma yana karanta ‘Ƙul Huwal Lahu Ahad’, sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Da wannan ne Aljanna ta tabbata a gare shi.” [Ahmad #16605].
• An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wani mutum ya tashi ya yi salla raka’a biyu na alfijir, a raka’ar farko ya karanta ‘Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’ sai Manzo Allah (ﷺ) ya ce: “Wannan bawa ne da ya san Ubangijinsa.” A raka’a ta biyu kuma sai ya karanta ‘Ƙul Huwal Lahu Ahad’, sai Annabi (ﷺ) ya ce: “Wannan bawa ne da ya yi imani da Ubangijinsa.” [Ibn Hibban #2460].
• An karɓo daga Naufal ɗan Mu’awiya Al-Ashja’i (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Ya Manzon Allah, koyar da ni abin da zan riƙa faɗa idan na zo kwanciya. Sai ya ce: “Ka karanta ‘Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun’ sannan ka yi barci bayan ka kai ƙarshenta, domin ita kuɓuta ce daga shirka.” [Ahmad #23807 da Abu Dawud #5055 da Tirmizi #3701 da Ibn Hibban #789, 790].
6. Babban Jigonta:
Tana tabbatar da Tauhidin kaɗaita Allah da bauta da nisantar shirka da raba hanya tsakanin Musulunci da sauran addinai.

***


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ ١ لَآ أَعۡبُدُ مَا تَعۡبُدُونَ ٢ وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ ٣ وَلَآ أَنَا۠ عَابِدٞ مَّا عَبَدتُّمۡ ٤ وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ ٥ لَكُمۡ دِينُكُمۡ وَلِيَ دِينِ ٦
【Tarjama】

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai
1. Ka ce: “Ya ku waɗannan kafirai.
2. “Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba.
3. “Ku kuma ba masu bautar abin da nake bauta wa ba ne.
4. “Ni kuma ba mai bauta wa abin da kuka bauta wa ba ne.
5. “Ku ma ba za ku bauta wa abin da nake bauta wa ba.
6. “Addininku na gare ku, ni ma kuma addinina na gare ni.”

【Tafsiri】

Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya fito sarari ya faɗa wa kafirai cewa, shi fa ko nan gaba ba zai bauta wa gumakan da suke bauta wa ba, su ma kuma a halin yanzu ba sa bauta wa abin da shi yake bauta wa, domin shi yana bautar Allah ne shi kaɗai, su kuma suna haɗa shi da wasu ababan bauta. Ya kuma ƙara tabbatar musu da cewa, shi a halin da ake ciki ba mai bautar abin da suke bauta wa ba ne, hakanan su ma ko nan gaba, ba masu bautar abin da yake bauta wa ne ba. Saboda haka ya shaida musu cewa, suna da addininsu na kafirci da suke bi, shi ma yana da nasa addini na Musulunci da yake kai, watau dai hanyar jirgi daban ta mota ma daban, ba za su taɓa haɗuwa ba.

『Daga wannana aya za mu fahimci abubuwa kamar haka:』

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Dole ne Musulmi su fahimtar da kafiran da suke zaune tare da su cewa, zama wuri ɗaya ba yana nufin su yi tarayya da su wajen ibadunsu ba, ko su saki nasu na addinin Musulunci su kama na waɗanda ba Musulmi ba, domin Musulunci ya wajabta wa ‘ya’yansa tsantsanta bauta ga Allah shi kaɗai ba tare da sanya masa abokin tarayya ba, amma duk sauran addinai sun gauraya da bautar wanin Allah.
2. Musulunci ba ya ɗaukar abin da mushirikan Larabawa suke yi bauta ce ga Allah, domin sun gauraya bautarsu da shirka, duk kuwa bautar Allah da aka haɗa ta da shirka, to a wurin Allah ba bauta ce karɓaɓɓiya ba, gara babu da ita.
3. Addinai duka a wurin Allah abu ɗaya ne, ba ruwansa da su, in ban da addinin Musulunci, shi ne kaɗai addini na gaskiya a wurin Allah.