114. Wane ne mafi zalunci kamar wanda ya hana masallatan Allah a riƙa ambaton sunansa a cikinsu, ya yi ta ƙoƙari wajen rushe su? Waɗannan bai kamata su shige su ba sai a cikin halin tsoro. Za su gamu da wulaƙanci a duniya a lahira kuma suna da wata azaba mai girma.
115. Gabas da yamma kuma na Allah ne. Duk inda aka fuskantar da ku to can ma alƙiblar Allah ce. Lalle Allah Mai yalwar falala ne, kuma Mai yawan sani.
A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) yana bayyana wanda ya fi kowa zalunci da ta’addanci cikin masu laifi, watau shi ne wanda ya hana bayin Allah ambaton Allah da bauta masa a masallatan Allah, ya tashi tsaye wajen rusa masallatan da lalata su. To irin waɗannan azzalumai, Allah ya sanya uƙubarsu ita ce, kada a bar su su shiga masallatan sai cikin halin tsoro da fargaba, watau lokacin da Allah ya ba wa muminai iko da galaba a kansu. Ko kuma ana nufin Allah zai jefa tsoro da firgici a zuƙatansu yayin da suka zo shiga waɗannan masallatai don gudun azabar da Allah zai jefa musu, duk da haka kuma suna tare da ƙasƙanci da kunya ta nan duniya, da kuma azaba mai girma a lahira da take jiran su.
Masana tafsirin Alkur’ani sun yi saɓani dangane da waɗanda Allah yake nufi a wannan aya, kamar haka:
1. Ayar tana magana ne a kan mushrikan Ƙuraishawa, waɗanda suka hana Annabi (ﷺ) da Musulmi shiga masallaci mai alfarma na Makka. Daga cikin masu wannan fahinta akwai Al-Hafiz Ibn Kasir [1:388] da Al-Allamah Ibn Ashur [1:678].
2. Wasu suka ce, ana nufin Nasara waɗanda suka taimaka wa Bukhtanassar (Nebuchadnezzar) wajen rushe masallacin Baitul Maƙadis da hana muminan Banu Isra’ila salla a cikinsa. Cikin masu wannan ra’ayi akwai Al-Imam Ibn Jarir [2:422].
3. Wasu kuma suna ganin ayar ta shafi duk wanda ya yi irin wannan aiki a da da yanzu har ma da nan gaba. Daga cikin masu wannan fahinta akwai Ibnu Aɗiyyah [1:199] da Ƙurɗubi [1:458].
4. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana girman mulkinsa da faffaɗan iliiminsa, da cewa duniya gaba ɗayanta gabas da yamma da abin da ke tsakaninsu, duk nasa ne, mulkinsa ne, don haka duk inda bawa ya fuskanta, to ya fuskanci fuskar Allah ne. Don haka yayin da mai salla ya kasa fayyace alƙiblar salla, ya yi iya ƙoƙarinsa wajen gano alƙibla, to nan ma a duk inda ya fuskanta ya yi sallarsa alƙiblar ce a wurin Allah, ko da kuwa ya kuskure wajen gano ta. Hakanan matafiyi yayin da zai yi sallar nafila a kan abin hawansa, to duk inda yake fuskanta nan ma alƙibla ce, kamar yadda ya zo a cikin sunnar Annabi (ﷺ). [Muslim #700].
***